2023: Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku

2023: Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku

  • Ba a ga Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers ba wurin taron gabatar da Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin Atiku a zaben shugaban kasa na 2023
  • Wike, shine ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar PDP na 2023 kuma yana cikin wadanda ake zaton zai iya zama mataimakin Atiku
  • Gwamnoni da suka hallarci taron sun hada da Ifeanyi Uguanyi na Enugu, Bala Mohammed na Bauchi; Udom Emmanuel na Akwa Ibom; Godwin Obaseki na Edo da Samuel Ortom na Benue

Ba a ga jigon jam'iyyar PDP kuma gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, a bikin gabatar da takwararsa na Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a zaben 2023, rahoton Leadership.

Idan za a iya tunawa Wike ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP da aka yi a ranar 28 na watan Mayu inda ya samu kuri'u 237 yayin da Atiku ya samu kuri'u 371.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Okowa, Atiku da Wike.
Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku a zaben 2023. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan zaben fidda gwanin, ana ta hasashen cewa Wike ne zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku saboda karfin fada aji da ya ke da shi a jam'iyyar.

Amma, Okowo ne aka gabatar a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ta PDP inda jiga-jigan jam'iyyar suka hallara a hedkwatarta a Abuja.

Ya ce wani abu da aka duba wurin zaben Okowa shine dacewarsa ya zama magajinsa idan an zabe shi shugaban kasa a 2023.

Jawabin Atiku Abubakar wurin taron gabatar da Okowa

"Na yi murnar sanar da Gwamna Ifeanyi A. Okowa a matsayin mataimaki na. Ina fatan jagorancin kasar mu tare, tare da yan Najeriya don gina gaba mai kyau gare mu baki daya," in ji Atiku.

Baya ga shugaban jam'iyyar na kasa Dr Iyorchia Ayu, mambobin kwamitin ayyuka, NWC, mambobin kwamtin amintattu, BOT, jiga-jigan jam'iyyar da takwarorin Okowa sun hallarci taron.

Sun hada da gwamnonin jihohin Enugu, Ifeanyi Uguanyi, Bauchi, Bala Mohamemd; Akwa Ibom, Udom Emmanuel; Edo, Godwin Obaseki, da Benue; Samuel Ortom.

Asali: Legit.ng

Online view pixel