2023: Da yuwuwar za'a ayyana gwamnan PDP mai ci a matsayin mataimakin Atiku

2023: Da yuwuwar za'a ayyana gwamnan PDP mai ci a matsayin mataimakin Atiku

  • Har yanzun jam'iyyun siyasa a Najeriya sun gaza samun matsaya kan waɗanda zasu kasance mataimakan yan takararsu na shugaban kasa
  • A ɓangaren babbar jam'iyyar hamayya PDP, alamu masu karfi sun nuna cewa gwamna Okowa na jihar Delta ke kan gaba
  • Hukumar INEC ta sanar da cewa jam'iyyu na da lokaci har zuwa ranar 17 ga watan Yuni, 2022 su kai mata sunayen yan takara

Abuja - Yayin da jam'iyyun siyasa ke kokarin cike gurbin mataimakan yan takararsu na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ɗan takarar PDP. Alhaji Atiku Abubakar, na gab da tsaida matsaya.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Punch cewa magoya bayan ɗan takaran na ƙunsa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin Atiku.

Matuƙar ba'a samu wani canji a lokacin karshe ba, Me yuwuwa Okowa za'a bayyana a matsayin mataimakin ɗan takara na sahun gaba a tseren ɗarewa kujera lamba ɗaya a 2023.

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
2023: Da yuwuwar za'a ayyana gwamnan PDP mai ci a matsayin mataimakin Atiku Hoto: Frank West/facebook
Asali: Facebook

Gwamna Okowa ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Atiku Abubakar a babban taron PDP na zaɓen ɗan takarar shugaban kasa wanda ya gabata a watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan ya ba gwamnan damar gabatarwa da fahimta cikin sauki ga Atiku, ban da wasu taimako da sadaukarwa da gwamanan ya yi wa ɗan takaran.

Wata majiya ta ce:

"Okowa ne ya haɗa kan kayan aikin da muka yi amfani da su a zaɓen fidda gwani, shi ne zaɓin da muka fi so duk da wasu na ganin a duba bai wa gwamna Wike da Udom."

A yanzun, bayanan da suka fito daga kwamitin jam'iyyar PDP, da ya ƙunshi gwamnoni, mambobin kwamitin ayyuka NWC, mambobin kwamitin amintattu BoT, ya nuna cewa a yau Talata za'a kawo ƙarshen wanda zai zama mataimaki.

Yayin da Jam'iyyar PDP ke martani kan lamarin ta bakin kakakinta, Debo Ologbunagba, ba ta bayyana ainihin lokaci ba amma ta nuna cewa lokaci zai yi alƙalanci bayan kammala shawara a makon nan.

Yaushe wa'adin INEC ke karewa?

A sanarwan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) jam'iyyun siyasa na da nan zuwa 17 ga watan Yuni, a matsayin rana ta ƙarshe ta miƙa mata sunayen yan takara da mataimakan su.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnoni 7 na APC kan zaɓo mataimakin Tinubu

Yayin da jam'iyya mai mulki ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimakin shugaban ƙasa, gwamnonin sun dira fadar Buhari.

Yanzu haka shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri da aƙalla gwamnoni Bakwai a fadarsa ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel