Bayan rashin nasara a zaɓen fidda gwani, Moghalu ya fice daga jam'iyyar ADC

Bayan rashin nasara a zaɓen fidda gwani, Moghalu ya fice daga jam'iyyar ADC

  • Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu, ya fice daga jam'iyyar ADC bayan rashin samun tikitin takara
  • Moghalu, a wata takarda da ya aike wa shugaban ADC, ya ce rashin adalcin da aka yi a zaɓen fidda gwani ne ya sa ya ɗauki wannan matakin
  • Ɗan takarar ya sha kaye ne a hannun Dumebi Kachikwu, yayin zaɓen fitar da gwani da ya gudana a Abeokuta

Abuja - Ɗan takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Kingsley Moghalu, ya yi murabus daga kasancewarsa mamba a jam'iyyar.

A wata takarda da ya aike wa shugaban jam'iyyar ADC, Okey Nwosu, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ce rashin adalcin da aka tafka a zaɓen fidda gwani ya sa ya bar ADC.

Dan takarar shugaban kasa, Kingsley Moghalu.
Bayan rashin nasara a zaɓen fidda gwani, Moghalu ya fice daga jam'iyyar ADC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa Moghalu na ganin an tafka rashin adalci a zaɓen duk kuwa da matakan da jam'iyya ta yi iƙirarin ɗauka don aiwatar da sahihin zaɓe.

Kara karanta wannan

Bayan kusan mako daya da shan ƙasa a zaben fidda gwani, Tsohon gwamna ya tura wa Tinubu sako kan zaɓen 2023

Wani sashin takardar murabus din ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na rubuta wannan takarda ne domin miƙa murabus ɗina daga jam'iyyar ADC nan take. Na yi haka ne saboda zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa da ya gudana a Abekuta ya nuna cin karo tsakani na da jam'iyya."
"Duk da jadawalin da kuka fitar kwanaki kaɗan kafin zabe wanda ya bayyana cewa jam'iyya zata ɗauki nauyin zuwa da wurin zaman Deleget a Abeokuta, wanda muka yi amanna kowane ɗan takara zai samu dama, ADC ƙarƙashinka ta gaza cika haka."
"Gazawar ku wanda ya nuna ƙarara cewa da gangan ne, ya hadda kace-nace da magana mara daɗi kan matakan da aka bi na yin zaɓen, wanda ya haɗa da ɗauke Deleget da ba su cin hanci."

Ɗan takarar ya ƙara da cewa wasu yan takara ciki har da shi kansa, sun ba da gudummuwar kuɗi ga asusun jam'iyya don ɗaukar nauyin deleget, amma komai ya canza.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Karon farko bayan lashe zaɓen APC, Tinubu ya lallaɓa ya sa labule da shugaban ƙasa

Wanene ya ci zaben fidda gwanin ADC?

Moghalu, wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaɓen 2019 karkashin jam'iyyar YPP, ya sha kaye a babban taron ADC na zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasan da ya gudana a Abeokuta.

Yayin da wanda ya samu nasara, Dumebi Kachikwu, ke da ƙuri'u 977, Moghalu ya samu kuri'u 589 a zaɓen, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma Wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya zabi wanda zai zama mataimakinsa a 2023

Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faɗi tashin neman mataimaki,Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA.

Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel