PDP: Tsohon Ministan Jonathan Ya Ci Zaben Fidda Gwani Na Sanata a Jigawa

PDP: Tsohon Ministan Jonathan Ya Ci Zaben Fidda Gwani Na Sanata a Jigawa

  • Dr Nuruddeen Muhammad, Tsohon karamin minista na harkokin kasar waje, ya lashe zaben fidda gwani na sanata a Jigawa
  • Muhammad ya yi nasarar zama dan takarar sanata na PDP ne ba tare da hammaya ba a zaben da aka yi a Hedeja a ranar Alhamis
  • Tsohon ministan ya mika godiyarsa ga daligets sannan ya yi kira ga al'ummar mazabarsa su tabbatar sun fito sun yi zabe don samun wanda zai wareware musu matsalolinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - Tsohon karamin minista na harkokin kasar waje, Dr Nuruddeen Muhammad, ya yi nasarar zama dan takarar sanata na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a Jigawa, rahoton Daily Trust.

Muhammad ya yi aiki ne a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

PDP: Tsohon Minista Ya Ci Zaben Fidda Gwanni Na Sanata a Jigawa
PDP: Tsohon Ministan Jonathan Ya Zama Dan Takarar Sanata a Jigawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

Tsohon ministan mai saka ido a Ma'aikatar Sadarwa na Tarayya ya samu tikitin ba tare da hamayya ba a zaben da aka yi a ranar Alhamis a Hadeja, Karamar Hukumar Hadeja a Jihar Jigawa.

Daily Trust ta rahoto, a jawabinsa na godiya, dan takarar ya mika godiyarsa da dukkan wakilan jam'iyya saboda karamcin da suka yi masa ya kuma bukaci masu zabe su tabbatar sun fito sun kada kuri'unsu saboda matsalolin da ke addabar mazabar.

Muhammad ya lissafa matsalolin da ya ke fatan zai warware wa al'umma idan an zabe shi a 2023

Ya lissafa matsalolin da suka hada da ambaliyar ruwa a kowanne shekara, kwarorowar hamada, yasar rafin Hadeja da yawan ciwon koda da wasu abubuwan.

Muhammad, shine dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar PDP a babban zaben shekarar 2015.

2023: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Sanar Da Wanda Zai Yi Wa Atiku Mataimaki

Kara karanta wannan

Tinubu: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba

A wani rahoton, Jam'iyyar APC da PDP, a ranar Alhamis sun bada himma wurin neman wadanda za su yi wa yan takarar shugabannin kasarsu mataimaki.

PDP ta kafa kwamiti wanda ya kunshi gwamnoninta, kwamitin ayyuka da kwamitin amintattu da tsaffin gwamnoni don zabo wanda zai yi wa jam'iyyar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Kwamitin ta yi taro a ranar Laraba da Alhamis a Abuja. Kakakin PDP, Debo Ologunaba, ya tabbatar wa The Punch kafa kwamitin a daren ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel