Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

  • Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Ahmed Wadada ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa
  • Wadada ya sanar da ficewarsa ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar APC na mazabar Tudun Kofa a Jihar Nasarawa
  • Tsohon dan majalisar ya ce rashin adalci da aka yi masa na canja ainihin sunayen daligets yayin zaben fidda gwani na yan majalisa ne yasa ya fice daga APCn

Jihar Nasarawa - Mr Ahmed Wadada, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, ya yi murabus daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

NAN ta rahoto cewa ya sanar hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban jam'iyyar APC, Tudun Kofa, karamar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa.

Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili
Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar APC. Hoto: @thecableng.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar ADC Ta Zabi Dan Takarar Shuagban Kasa, Ya Yi Alkawarin Yi Wa Tinubu Da Atiku Ritaya

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ga wasikar mai dauke da sa hannun Wadada a ranar Laraba.

Wadada, a cikin wasikar mai kwanan wata na 1 ga watan Yunin 2022, ya ce ya dauki wannan matakin ne sakamakon zaben da aka yi a Nasarawa West inda ya janye duk da cewa shine ke kan gaba.

Dalilin da yasa na yi murabus daga APC, Wadada

Ya ce rikicin na da alaka da canji da aka yi a ainihin sunayen daliget na zabe, wanda ya ce hakan ya saba wa ka'idar demokradiyya.

Wasikar ta Wadada:

"Ni Honarabul Ahmed Wadada Aliyu mai lambar rajista NW/KEF/06/01001, ina son rubuta cewa zan yi murabus daga jam'iyyar APC.
"Na yanke wannan hukuncin ne saboda rashin bin doka da aka yi da ya saba wa demokradiyya a zaben cikin gida na kujerar sanata ta Nasarawa West, bayan na tuntubi yan mazaba ta da abokaina na na siyasa.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

"Ina maka gaisuwa da fatan a huta lafiya."

2023: Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da gwamnoni da aka zaba a karkashin jam'iyyar.

Wasu majiyoyi da suke da masaniya kan taron sun shaida wa Vanguard cewa wannan taron shine na farko cikin taruruka da za a yi don shirin kamfen din babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel