Tinubu: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba

Tinubu: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya ce dole a hana PDP komawa kan mulki
  • Tinubu ya furta hakan ne yayin da ya ke jawabinsa bayan an sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na fidda gwani na APC a ranar Laraba
  • Tinubu ya ce jam'iyyar na PDP ta shafe shekaru 16 tana tafka barna a bangarori daban-daban a Najeriya don haka dole a hana su samun ikon taba baitul malin Najeriya

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben shekarar 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce dole jam'iyyarsa ta yi iya kokarinta don ganin PDP bata karbi mulki ba, Daily Trust ta rahoto.

A zaben fidda gwani na jam'iyyar ta APC da aka kammala a ranar Laraba, Tinubu ya samu kuri'u 1,271, mafi rinjaye ya kuma yi nasara.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

2023: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba, Tinubu
Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Komawa Kan Mulki Ba, Tinubu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai biye masa, Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri ya samu kuri'u 316. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samu kuri'u 235, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya samu kuri'u 152. Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya samu kuri'u 47.

Bayo Onanuga, direktan sadarwa na kwamitin kamfen din Tinubu, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ambaci dan siyasan yana ambatar hakan a jawabinsa na amincewa da nasararsa, rahoton Nigerian Bulletin.

Ya zama dole mu tabbatar PDP ba ta koma kan mulki ba a 2023, Tinubu

Tinubu ya ce ya zama dole jam'iyyar ta yi aiki don ganin PDP bata dawo kan mulki ba bayan shekaru 16 tana lalata kasa.

"Sun lalata tattalin arzikin mu. Sun bar ayyuka ba su kammala ba. Ayyuka nawa suka bari ba su kammala ba? Dole mu hana su taba makullin baitil malin mu. Dole a hana PDP dawowa kan mulki," in ji shi.

Kara karanta wannan

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

Tinubu ya mika godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, Matar Shugaban kasa, Aisha Buhari, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, yan majalisa bisa goyon bayansu da sauran abokan takararsa da wadanda suka janye masa.

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

A wani rahoton, Abdullahi Ganduje, gwamnan Jihar Kano, ya taya Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, murnar samun nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar APC, rahoton The Cable.

Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya doke abokan fafatawarsa a zaben na fidda gwani da aka kammala a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

A cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren watsa labarai, Ganduje ya ce nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel