Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

  • Yayin da ake ci gaba da gwabza zaben fidda gwani a APC, sanata kuma shugaban masu rinjaye ya bar APC
  • Rahoton na zuwa ne kwanaki bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwanin gwamna na APC a jihar Kebbi
  • Sanata Yahaya Abdullahi dai ya sanar da komawa jam'iyyar PDP ta bakin mai magana da yawunsa

Kebbi - Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi, inji Punch.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Jamil Gulma, wanda ya tabbatar da sauya shekar ya fitar da sanarwa.

Yahaya Abdullahi, shugaban masu rinjaye ya bar APC, ya koma PDP
Yanzu-Yanzu: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito shi yana cewa:

“Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba domin shelanta shiga jam’iyyar PDP, kuma zai nuna sha’awar sa ta tsayawa takarar kujerar a yanzu.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babbar Kotu ta soke zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dokta Yahaya wanda ya halarci zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC bai samu kuri'a ko daya ba, sakamakon da ya ki amincewa da shi kuma ya bayyana shi a matsayin wasan kwaikwayo kuma wasan yara.

Masu fashin baki dai sun ce ficewar tasa ba za ta rasa nasaba da zaben fidda gwanin takarar gwamnan da wasu da dama a shugabannin jam'iyyar APC mai mulki suka yi masa makarkashiya ba.

Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari

A wani labarin, 'yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas sun rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), domin bai wa yankin Kudu maso Gabas damar fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce

A wani kwafin wasikar da wakilin Punch ya samu a ranar Talata, ‘yan takarar sun bukaci Buhari ya sa baki a yayin zaben domin samar da “shugaba mai kyau”.

Wasikar na dauke da sa hannun Ikeobasi Mokelu, tsohon ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Dokta Ogbonnaya Onu; karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da Mrs. Ken Uju-Ohanenye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel