Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari

Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari

  • 'Yan takarar shugaban kasa na APC daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun bayyana bukatar Buhari ya goyi bayansu
  • Sun bayyana haka ne daidai lokacin da ake ci gaba da ba Buhari zabin da ya kamata ya duba domin amincewa dashi
  • Ya zuwa yanzu dai za a fara zabe, kuma ana sa ran kammala shi zuwa daren yau dinnan kamar yadda rahotanni suka bayyana

'Yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas sun rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), domin bai wa yankin Kudu maso Gabas damar fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

A wani kwafin wasikar da wakilin Punch ya samu a ranar Talata, ‘yan takarar sun bukaci Buhari ya sa baki a yayin zaben domin samar da “shugaba mai kyau”.

Kara karanta wannan

'Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Guda 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari

'Yan Kudu na neman a basu tikitin takara
Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari
Asali: Original

Wasikar na dauke da sa hannun Ikeobasi Mokelu, tsohon ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Dokta Ogbonnaya Onu; karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da Mrs. Ken Uju-Ohanenye.

An saka Sanata Rochas Okorocha a cikin wadanda za su sanya hannu amma bai sanya hannu ba, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gargadi jam'iyyar APC, cewa cire sunansa a jerin 'yan takarar shugaban kasa da za su gwabza a zaben fidda gwani na yau daidai yake yake da kunno wutar rikici, Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Bello, wanda yana daya daga cikin ’yan takara 23 a jam’iyyar, ya ce akwai makarkashiyar da ake shirya masa, inda ya zargi gwamnonin APC na Arewa da wasu jiga-jiga da kitsa manakisa akansa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock

Bello wanda ya bayyana kansa a matsayin dan takara mafi karbuwa da zai yi nasara idan har tsarin ya tafi daidai, ya ce abu daya ne zai hana shi ya tsaya takarar shugaban kasa shi ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya janye daga takarar, inji The Nation.

An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku

A wani labarin, Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun kara rage jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben fidda gwanin shugaban kasa zuwa uku, rahoton Vanguard.

Da sanyin safiyar Talata ne gwamnonin suka gabatar da jerin sunayen mutane biyar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a tantance su saboda a cimma matsaya daya.

Wadanda aka fara gabatar da su ga Buhari su ne: ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi; Gwamna Kayode Fayemi da Gwamna Dave Umahi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rikici a APC yayin da ake yunkurin magudi a jerin sunayen deliget

Asali: Legit.ng

Online view pixel