Yanzu-Yanzu: An matsaya wa Osinbajo lamba ya janye Bola Tinubu takara

Yanzu-Yanzu: An matsaya wa Osinbajo lamba ya janye Bola Tinubu takara

  • Yankin kudu maso yammacin Najeriya na kokarin ganin an kawo karshen rikicin neman tikitin takarar shugaban kasa a APC
  • Wasu bayanai sun nuna cewa yan takara sun zama biyu, kuma Sarakuna sun matsawa Osinbajo lamba ya janye wa Bola Tinubu
  • Wani jigon APC ya tabbatar da cewa ana cigaba da gudanar da tarurruka kuma idan komai ya yi kyau nan gaba kaɗan za'a zo ƙarshe

Abuja - Faɗi tashi da ƙoƙarin rage yawan adadin yan takarar shugaban ƙasa a APC ya ɗauki sabon babi, yayin da shugabannin kudu maso yamma da suka haɗa da sarakuna suka matsa wa Yemi Osinbajo ya janye wa Bola Tinubu.

Hakanan kuma wssu bayanai na cewa ana cigaba da kokarin shawo kan gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti don ya janye wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, vanguard ta ruwaito.

Bola Tinubu tare da Osinbajo.
Yanzu-Yanzu: An matsaya wa Osinbajo lamba ya janye Bola Tinubu takara Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Daga cikin yan takara biyar da gwamnonin arewa tare da kwamitin gudanarwa NWC suka shawarci a zaɓi ɗaya, Gwamna Fayemi, Osimbajo da Tinubu duk yan kudu maso yamma ne.

Sauran sun haɗa da Rotimi Amaechi wanda ya fito daga yankin kudu maso kudancin ƙasa, sai kuma gwamna Dave Umahi daga kudu maso gabashin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fayemi, wanda ke kan kujerar shugaban kungiyar gwamnonin ƙasa NGF, bayanai sun nuna cewa yana taƙama da goyon bayan takwarorinsa gwamnoni.

Mafi yawan gwamnoni waɗan da ake zargin suna hangen kujerar mataimakin shugaban ƙasa na tare da Bola Tinubu, yan kalilan na tare da Osinbajo.

Kudu maso yamma na kokarin haɗa kai wuri ɗaya

Wata majiya ta ce jagororin yankin kudu maso gabas na kokarin tsayar da ɗan takara ɗaya, don haka suka matsa wa Osinbajo da Fayemi su janye su barwa Bola Tinubu.

Wani jigon APC ya faɗa wa jaridar cewa:

"Ana cigaba da taruka kuma idan har suka fitar da sakamako mai kyau zai rage saura yan takara biyu, hakan zai sa kammala zaɓen cikin ƙanƙanin lokaci."

A wani labarin kuma Jam'iyyar NNPP ta sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan Katsina

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023.

Injiniya Muhammad Nuru Khalil shi ne ya lashe tikitin NNPP bayan samun nasara kan abokin takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel