Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba

Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba

Da wannan sauye-sauye da aka samu a siyasar Najeriya gabannin babban zaben 2023, akwai shakku sosai idan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai samu tikitin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Akwai rahotannin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya son sa a matsayin magajinsa. Wasu masu ruwa da tsaki suna tsoron cewa Tinubu wanda ke fada aji sosai a siyasa zai yi tsauri sosai idan ya samu mulkin shugabancin kasar.

Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba
Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Idan tsohon gwamnan na jihar Lagas ya gaza samun tikitin shugaban kasa na APC, akwai wasu matakai uku da zai iya dauka:

Ci gaba da kasancewa a APC da goyon bayan wanda ya yi nasara

Sauya sheka ba sabon abu bane a siyasar Najeriya. Sai dai kuma, sabanin takwarorinsa da dama, ba a san Tinubu da sauye-sauyen sheka daga wannan jam’iyyar siyasar zuwa wata ba. Maimakon haka, yana gina jam’iyyun siyasa da kulla kawance da wasu jam’iyyun.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Don haka, idan za a yanke hukunci daga yadda ya saba, Tinubu na iya zabar ci gaba da kasancewa a APC sannan ya marawa duk dan takarar da ya lashe tikitin shugaban kasa na APC idan har ya sha kaye bisa adalci.

Kwanan nan, tsohon gwamnan na jihar Lagas ya magantu game da abun da zai yi idan ya sha kaye a zaben fidda gwani.

A wani bidiyo da hadimin Gwamna Babajide Sanwo Olu, Jubril Gawat, ya wallafa a twitter a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, Tinubu wanda ya yi magana cikin harshen Yarbanci ya ce zai amshi kaye idan ya fadi.

"Idan suka kayar da ni, zan koma gida," in ji tsohon gwamnan jihar Legas a cikin harshen Yarbanci.

Tsayawa a APC amma aiki tare da Atiku na PDP ta karkashin kasa

Kara karanta wannan

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

Kasancewarsa mai fada aji a APC, jam’iyyar da shi ya taimaka wajen kafa ta, ya kashe mata kudi sannan ya raineta ta zama abun da take a yau, Tinubu na iya kin sauya sheka koda kuwa yana ganin an cuce shi a zaben fidda gwani.

Sai dai kuma, yana iya yanke shawarar yin aiki don nasarar dan takarar wata jam’iyya a matsayin hanyar hukunta jam’iyyarsa.

Idan Tinubu ya yanke hukuncin bin wannan hanyar, yana iya dinkewa da dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Yan siyasar biyu sun kasance makusanta na dogon lokaci, Tinubu ya baiwa Atiku jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) don ya nemi takarar shugaban kasa a karkashinta a 2007.

Idan Tinubu ya yanke shawarar aiki da Atiku yayin da yake ci gaba da kasancewa APC, hakan ba zai zamo karo na farko da tsohon gwamnan na Lagas zai aikata haka ba.

A 2011, an rahoto cewa ya kulla yarjejeniya da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan don kawo ma jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin jihohin kudu maso yamma yayin da yake masayin shugaban ACN.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Sauya sheka zuwa wata jam’iyyar

Idan Tinubu ya gaza samun tikitin shugaban kasa na APC, yana iya ganin an yaudare shi sannan ya yanke shawarar komawa wata jam’iyyar don cimma dadaddiyar burinsa.

Akwai rahotannin cewa shugaban na APC yana da mafita kuma zai sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) idan bai samu tikitin APC ba.

Sai dai kuma, tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigon SDP, Segun Oni, ya bayyana rahoton a matsayin hasashe kawai.

Sai dai kuma wani na hannun daman tsohon gwamnan Legas wanda bai bayyana sunansa ba ya ce zai iya neman wasu mafitan idan zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC bai kasance bisa gaskiya da adalci ba.

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

A wani labarin kuma, babban jagoran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen juyin mulki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Lamido ya ce wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel