2023: Jam'iyyar PRP ta sanar da sakamakon zaɓen ɗan takararta na shugaban kasa
- Jam'iyyar PRP ta sanar da ɗan takararta na shugaban ƙasa wanda zai fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe
- Kola Abiola, shi ne wanda ta bayyana ya lashe tikitin kujera lamba ɗaya na PRP bayan lallasa abokan takara da gagarumin rinjaye
- Haka nan jam'iyyar ta kuma tsayar da wanda zai fafata a babban zaɓen gwamnoni da ke tafe a jihar Kano
Abuja - Jam'iyyar Peoples Redemption Party wato PRP ta sanar da sakamakon fidda gwani na takarar shugaban ƙasa wanda ya gudana ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Zaɓen, wanda ya gudana a babbar Sakatariyar PRP ta ƙasa da ke Abuja, ya nuna cewa Kola Abiola, shi ne ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.
Shugaban PRP na ƙasa, Falau Bello, ya ce Abiola ya samu gagarumar nasara da kuri'u 2,097 inda ya lallasa babban abokin hamayyarsa Alhaji Usman Bugaje, wanda ya samu kuri'u 813.
Sai kuma Patience Ndidi dake bin bayan mutum biyu da kuri'u 329, yayin da Gboluga Mosugu ya biye musu baya da kuri'u 263.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sakamakon ya fito ne daga jihohin da Deleget suka samu damar kaɗa kuri'u kuma aka tura zuwa babbar Sakatariya domin sanarwa ta ƙarshe.
A sakamakon da jam'iyyar ta sanar da ranar Lahadi da daddare ya nuna cewa Deleget 3522 aka tantance zasu kaɗa kuri'a yayin da kuri'u 3416 suka inganta, 141 suka lalace.
Dalilin da yasa muka gudanar da zaɓen a jihohi - PRP
Tun a jawabinsa na farko, Bello ya ce jam'iyyar PRP ta aiwatar da zaɓen fiid da gwaninta daban da sauran jam'iyyu saboda tana son sauƙaƙa wa mutane ta hanyar kai lamarin kusa da su.
Wanda ya lashe tikitin takarar, Kola Aboila, ɗa ne ga Chief Moshood Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 amma Janar Ibrahim Badamasi Babamgida ya soke shi.
PRP ta sayar da ɗan takarar gwamnan Kano
Haka nan kuma, PRP ta ayyana Salihu Tanko Yakasai, a matsayin wanda ya ciri tura kuma ya lashe tikitin takarar gwamnan Kano a zaɓen da ta gudanar.
A wani labarin kuma Daga Ƙarshe, Shugaban Buhari zai faɗi sunan wanda yake son ya gaje shi a 2023, zai gana da yan takara
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta fallasa wasu shirye-shiryen Buhari gabanin zaɓen fidda gwanin APC.
Bayanan sun ce Buhari zai gana da dukkanin yan takarar jam'iyyar APC kuma zai bayyana wanda yake goyon bayan ya gaje shi.
Asali: Legit.ng