Yanzu-Yanzu: Dandazon jama'a tarbi Tambuwal a Sokoto bayan zaben fidda gwanin PDP

Yanzu-Yanzu: Dandazon jama'a tarbi Tambuwal a Sokoto bayan zaben fidda gwanin PDP

  • Bayan kammala zaben fidda gwanin PDP, gwamna Tambuwal ya dawo gida, ya samu tarbar dandazon masoyansa
  • A yammacin yau ne aka ce gwamnan ya dura a filin jirgi, inda jama'a da dam suka hallara domin tarbarsa
  • Idan baku manta ba, Aminu Tambuwal ya janyewa Atiku a zaben fidda gwani, kana ya nemi magoya bayansa su zabi Atiku

Jihar Sokoto - Dandazon jama'a ne suka yi maraba da dawowar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Punch ta ruwaito.

Tambuwal ya janye daga takara ne a ranar Asabar din da ta gabata, ya kuma bukaci magoya bayansa da su zabi Atiku Abubakar, wanda a karshe ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar

Tambuwal ya dawo Sokoto
Yanzu-Yanzu: Dandazon jama'an tarbi Tambuwal a Sokoto bayan zaben fidda gwanin PDP | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Jama'ae sun yi ta rera waka da raye-raye yayin da suka shiga ayarin motocin gwamnan zuwa cikin birnin daga filin jirgi, This Day ta ruwaito.

An bayyana ci gaban a matsayin wanda ya sauya sheka da ya sa Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel