'Karin Bayani: Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola Tinubu

'Karin Bayani: Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma daya cikin masu neman takarar shugabancin kasa ya ce bai zai taba furta kalamai na cin mutunci ga Shugaba Buhari ba
  • Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ce ba a fahimci abin da ya ke nufi bane yayin da ya ke yi wa daliget na Jihar Ogun jawabi ya kuma ce ba domin shi ba da Buhari bai ci zabe a 2015 ba
  • Tinubun ya ce yana alfahari da gudun mawar da ya bada wurin kafuwar APC da gina ta amma Shugaba Muhammadu Buhari shine jagorar nasararsa kuma iya rike kasa da ya yi na shekaru bakwai abin jinjina ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas kuma mai neman takarar shugabancin kasa a APC, ya ce ba zai dace ya ci mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari ba, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar game da jawabinsa yayin ganawa da deliget a Jihar Ogun.

Yanzu: Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu Ta Janye Maganganunsa Kan Buhari, Ta Ce Ba a Fahimce Shi Bane
Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu Ta Janye Maganganunsa Kan Buhari, Ta Ce Ba a Fahimce Shi Bane. @Mobile_Punch.
Asali: Twitter

A wurin taron, mai neman takarar shugaban kasar ya ce ba domin shi ba da Buhari ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma cikin wata sanarwar da ya fitar domin karin haske, Tinubu ya ce ba yi nufin rashin girmama wa ga Buhari.

Ina alfahari da rawar da na taka wurin kafuwar APC da nasarorinta, Amma Buhari, tabbas, shine jagora a nasarar," in ji tsohon gwamnan.

"An zabe shi shugaban kasa sai biyu. Ya rike kasa da gwamnati na tsawon shekara bakwai. Babu abinda zai canja hakan. Ba zan raina shi ba ko abin da ya yi wa jam'iyya da kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari dan Arewa ya dana mulki shekara 8, 2023 ta mu ce, mu Yarbawa

Kungiyar yakin neman zaben Tinubu ta yi karin bayani game da jawabinsa

Kungiyar yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta ce kafafen watsa labarai ba su fahimci kalaman da dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi ba, rahoton The Punch.

The Punch ta rahoto cewa Tinubun, yayin ganawa da daligets na APC a Jihar Ogun ya bugi kirji kan cewa shine ya yi sanadin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Ogun Dapo Abiodun da wasu suka zama abin da suka zama a yau a siyasa.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Direktan Watsa Labarai na kungiyar yakin neman zabe, Bayo Onanuga, a ranar Juma'a, ya ce bayyana rahotonin jawabin Tinubu a matsayin abu mai cike da "kura-kurai da mugun nufi."

Onanuga ya ce abin da Tinubu ya fada abubuwa ne da kowa ya sani kuma gaskiya ne wanda an dade ana nazarinsu tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Hotuna: Daga karshe, an yiwa Ibrahim Magu karin girma zuwa AIG

2023: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya, In Ji Bola Tinubu

A wani rahoton, Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, a ranar Alhamis ya ce shine ya cancanci ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari saboda idan aka yi la'akari da abubuwan da ya yi a baya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai Abeokuta domin neman goyon bayan daligets gabanin zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na APC, Vanguard ta rahoto.

Jagoran na APC wanda ya yi magana cikin harshen yarbanci, ya tunatar da su irin rawar da ya taka wurin gina jam'iyyar APC har ta zama jam'iyya mai mulki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel