Na hango nasara ne, shiyasa na rabu da Saraki, na bi layin Atiku a PDP inji Dino Melaye

Na hango nasara ne, shiyasa na rabu da Saraki, na bi layin Atiku a PDP inji Dino Melaye

  • Ana zargin Dino Melaye da cewa ya juyawa Bukola Saraki baya a 2023, ya bi layin Atiku Abubakar
  • Melaye bai goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar PDP ba
  • Tsohon Sanatan ya ce dalilin yin hakan shi ne Atiku zai samu gwaggwabar nasara a zabe mai zuwa

Abuja - Tsohon Sanatan Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya bayyana cewa yana goyon bayan Atiku Abubakar ne domin shi zai ci zabe.

Da aka zanta da shi a wani shiri a gidan talabijin na TVC, Sanata Dino Melaye ya yi ikirarin Atiku Abubakar zai samu gagarumar nasara a zabe na 2023.

‘Dan siyasar yana sa ran ‘dan takarar shugaban kasar na PDP zai ba sauran jam’iyyu tazara mai yawa a zaben sabon shugaban kasa na shekarar badi.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa

A cewar fitaccen ‘dan majalisar, an yi adalci da gaskiya a zaben fitar da ‘dan takaran shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta gudanar a makon da ya wuce.

Ya aka yi Dino ya bar Saraki?

Melaye ya amsa tambaya a game da dalilinsa na goyon bayan Atiku Abubakar a PDP, bayan kuwa da farko an san cewa yana cikin yaran Bukola Saraki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan ya bayyana cewa bai canza gida ba, kuma a lokacin da yake goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, ya yi masa biyayya 100%.

Dino Melaye
Dino Melaye, Atiku Abubakar da Bukola Saraki Hoto: Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

“Ban canza sheka daga goyon bayan Saraki zuwa Atiku ba. Na kasance ina goyon bayan Saraki 100% a lokacin da na ke tare da shi.”
“Ba ni da wata matsala da Saraki, ko a yau da safe na hadu da shi, mu ka sha dariyanmu.”

Kara karanta wannan

Sakon Obi ga matasan Najeriya: Ya rataya a wuyanku ku kori PDP da APC a 2023

Ana bukatar mai hada kan mutane

“Wannan karo na zabi Atiku ne domin dole in yi tarayya da wanda kowa ya san shi. A yanzu ana bukatar wanda zai hada-kan Najeriya.”
“Ba a bukatar wanda ake yi wa kallon Musulmi ko Kirista. Atiku mutum ne da ya shahara, wanda babu inda sunansa bai shiga a kasa ba."
“Don na tashi daga wajen wanda ba a san da shi ba, zuwa wajen wanda aka sani, ban canza gida ba, na bi wanda zai iya gyara Najeriya ne.”

- Dino Melaye

Punch ta rahoto Melaye yana cewa jam’iyyarsa ta PDP za ta iya karbe mulki daga hannun APC domin Atiku yana da lafiya da basira, kuma ya kware a siyasa.

Yamutsi a gidan APC

Ku na da labari cewa Gwamnoni biyar sun saye fam din takarar shugaban kasa, amma da alama dukkansu ba za su kai labari a zaben fitar da gwanin APC ba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

Manyan masu neman takaran su na neman daurin gindi da kamun kafa a wajen wadanda suka shaku da Muhammadu Buhari domin su samu tikitin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel