2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa

2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa

  • Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Farouk Aliyu, ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da shugabancin kasar a 2023
  • Aliyu ya ce jam’iyyar na da akalla yan takarar shugaban kasa biyar da za su iya kayar da Atiku idan har suka mallaki tikiti a 2023
  • Sai dai kuma, ya yarda cewa ba za a iya raina karfin dan takarar na PDP kuma tsohon shugaban kasar ba

Farouk Aliyu, tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na da yan takara biyar da za su iya lallasa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ne ya mallaki tikitin PDP na babban zaben 2023 mai zuwa bayan ya kasar da babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu

2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa
2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Chibuike R Amaechi, Chukwuemeka Nwajiuba, Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

A wata hira da Channels TV, Aliyu ya lissafa yan takara hudu cikin biyar da yake ganin za su iya kayar da Atiku idan suka lashe tikitin jam’iyyar mai mulki.

Yan takarar sune:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

  1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
  2. Asiwaju Bola Tinubu
  3. Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
  4. Tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba

Ya ce:

“Muna da mutane fiye da guda biyar a APC da za su iya kayar da Atiku Abubakar, Amaechi, Bola Tinubu, Emeka Nwajiuba, mataimakin shugaban kasa Osinbajo za su iya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng