Tashin hankali: 'Yan APC sun tada hankali saboda kakaba musu 'yar takara a wata jiha

Tashin hankali: 'Yan APC sun tada hankali saboda kakaba musu 'yar takara a wata jiha

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu mazauna a jihar Legas sun tada hankali kan yadda shugabannin APC suka zaba musu 'yan takara
  • Yayin da suke bayyana rashin jin dadinsu ga zaban wata mata, sun koka cewa, Tinubu da sauran shugabannin APC ba su kyauta musu ba
  • Sun kuma zargi cewa, an dauko wadanda basu ci zaben fidda gwani ba sun karbi tikitin jam'iyyar a yankunansu

Mambobin jam’iyyar APC a karamar hukumar Kosofe da ke jihar Legas, sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kakaba musu ‘yan takara a zaben 2023 a zaben fidda gwani da aka kammala a jihar kwanan nan.

Masu zanga-zangar sun yi watsi zabo Hajia Kafilat Ogbara, wacce ta yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazabar Kosofe ta majalisar tarayya, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu

Yadda rikici ya barke a Legas saboda kakaba musu 'yar takara
Tashin hankali: 'Yan APC sun tada hankali saboda kakaba musu 'yan takara a wata jiha | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ogbara Kafilat, tsohuwar kwamishiniya a hukumar binciken kudi ta jihar Legas, ta samu kuri’u 44 inda ta doke abokin hamayyarta kuma mai ci a majalisar Hon. Rotimi Agunsoye, wanda ya samu kuri'a daya.

Masu zanga-zangar dai sun zargi jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar da hannu wajen kakaba musu wasu ‘yan takara da basi gamasu dasu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan jam’iyyar da suka mamaye tituna ranar Alhamis, sun yi zargin cewa shugabannin jam’iyyar sun yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi, maimakon haka suka daura ‘yan takarar da suka fadi.

Sun dauki kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban da ke nuna rashin amincewarsu ga wannan zabe da aka gudanar, rahoton Premium Times.

Daya daga cikinsu ya ce:

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

“Mun yi imani da daidaito, adalci da gaskiya, ya kamata shugabanninmu su zo su yi bayanin abin da ya faru saboda ba mu zabi Kafilat ba. Na shaida zaben a unguwanni bakwai kuma mun zabi ‘yan takararmu amma ba mu san abin da ya faru ba a bayan fage."

Ya kuma bayyana cewa, babu amfanin dimokradiyya idan har shugabanni za su kakaba 'yan takara ga al'umma.

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

A wani labarin, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kai ga hayewar shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015.

Tinubu ya kuma ce shi ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana ne a dakin taro namasaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget din jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

Asali: Legit.ng

Online view pixel