Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu

Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu

Gabannin babban zaben 2023, gwamnoni guda bakwai ne suka samu tikitin jam’iyyarsu domin shiga tseren kujerar majalisar dattawa.

Al’ada ce a tsakanin gwamnonin Najeriya komawa majalisar dattawa da zaran sun kammala wa’adin mulkinsu guda biyu (shekaru takwas).

Ga gwamnonin da ke da ra’ayin ci gaba da mulki amma basu da tabbacin samun mukamin minista, su kan kama majalisar dattawa a matsayin mafita, don ganin an ci gaba da damawa da su a siyasa.

Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu
Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

A wannan zauren, Legit.ng za ta tattauna kan gwamnonin da suka yi nasarar mallakar tikitin takarar sanata a jam’iyyarsu gabannin babban zaben mai zuwa.

1. Ifeanyi Ugwuanyi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya yi nasarar kayar da masu neman takara uku wajen lashe tikitin sanata mai wakiltan Enugu ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

2. Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom shine zai daga tutar jam’iyyar PDP a zaben sanata mai wakiltan Benue ta arewa.

3. Darius Ishaku

Gwamnan jihar Taraba wanda ke shirin kammala wa’adinsa na biyu a 2023, Darius Ishaku ya yi nasarar mallakar tikitin takarar kujerar sanata mai wakiltan Taraba ta kudu a babban zabe mai zuwa.

4. Okezie Ikpeazu

Gwamna Okezie Ipeazu na jihar Abia shine zai daga tutar PDP a zaben sanata mai wakiltan yankin Abia ta kudu a zaben 2023.

5. Atiku Bagudu

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi wanda ke gab da kammala wa’adinsa na biyu ya yi nasarar cafke tikitin APC na zaben sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya.

6. Abubakar Sani Bello

Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello ya yi nasara a zaben fidda dan takarar sanata mai wakiltan Niger ta arewa karkashin inuwar jam’iyyar APC.

7. Simon Lalong

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong shine zai daga tutar jam’iyyar APC a zaben sanata mai wakiltan Plateau ta kudu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

A wani labarin, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic party (PDP) a zaben gwamnan jihar Borno na 2023, Mohammed Jajare, ya zargi gwamnan jihar, Babagana Zulum na baiwa abokai, iyalai da yan uwansa kwangiloli ta hanyar fakewa da aiki kai tsaye.

Jajare ya kuma yi zargin cewa gwamnan na siye manyan yan PDP a jihar don kawar da adawa a jihar.

Da yake zantawa da jaridar The Punch a ranar Lahadi, Jajare ya bayyana cewa tsawon shekaru gwamnati mai ci a Borno ta fitar manyan masu fada aji daga PDP don ci gaba da tsarin jam’iyya daya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel