Jigon APC ya bayyana sunayen yan takara 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023

Jigon APC ya bayyana sunayen yan takara 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023

  • Honorabul Farouk Aliyu ya ce akwai yan takarar shugaban ƙasa sama da 5 a APC da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023
  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya ce Atiku ba kanwar lasa bane da zasu saki jiki, zasu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara
  • Ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na kokarin zakulo wani ɗan takara da yan Najeriya zasu ƙaunace shi

Abuja - Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin tarayya, Farouk Aliyu, ranar Laraba, ya ce APC na da akalla yan takarar shugaban ƙasa biyar da zasu lallasa ɗan takarar PDP a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP bayan ya lallasa babban mai mara masa baya, gwamna Wike na Ribas.

Kwana huɗu bayan taron fitar da gwanin PDP, Farouk Aliyu, ya ce jam'iyya mai mulki a ankare take kuma tana kula don tsaida wanda zai lallasa tsagin hamayya, APC ta cigaba da jan zarenta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yan Najeriya sun waye Atiku ba zai samu kuri'u Miliyan 11m ba, Kwankwaso

Tsohon shugaban marasa rinjaye. Farouk Adamu Aliyu.
Jigon APC ya bayyana sunayen yan takara 5da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023 Hoto: labarai24.com
Asali: UGC

Wane yan takara ne a APC zasu kada Atiku?

Da yake zantawa da kafar Talabijin ta Channels tv cikin shirin 'Siyasa a yau' Jigon ya lissafo yan takara da suka haɗa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu ya ƙara da sunayen Jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, tsohon ƙaramin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, da wasu da yake ganin wuyan su ya kai su kalubalanci Atiku a zaɓe.

Sai dai ya amince da cewa ɗan takarar da PDP ta tsayar ba kanwan lasa bane da zasu yi watsi da shi duba da shaharar da ya yi a dukkan sassan ƙasar nan.

A kalamansa ya ce:

"Muna da yan takara sama da biyar da zasu iya kai Atiku Abubakar ƙasa a zaɓe; Amaechi, Bola Tinubu, Emeka Nwajiuba da mataimakin shugaban ƙasa duk zasu iya."

Kara karanta wannan

2023: Kar ku ɗauka kwace mulki hannun APC abu ne mai sauƙi, Atiku ya gargaɗi PDP

"Mafi yawan masu neman takarar mu na APC zasu iya lallasa Atiku Abubakar, mu ke da mulki ba zamu zauna mu kama hannu muna kallon abubuwa na faruwa ba, aiki zamuyi tukuru, yan Najeriya zasu zaɓi APC.

Ko tsayar da Atiku zai tilasta wa APC zakulo ɗan arewa?

Yayin da aka tambaye shi ko tsaida Atiku ya tilasta wa APC nemo zakakurin ɗan takara daga Arewa. Aliyu bai amsa tambayar kai tsaye ba, ya ce wasu shugabannin APC na kokarin nemo jajirtaccen ɗan takara.

A cewarsa, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a matsayin uban jam'iyya, yana duba jajirtaccen ɗan Najeriya wanda mutane zasu aminta da shi.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan gwamnonin APC yayin da yake shirin zaɓar ɗan takarar da yake fatan ya gaje shi a 2023.

Kara karanta wannan

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

Yayin ganawarsa da gwamnonin kafin tafiyarsa Sufaniya, Buhari ya ce zai duba wasu muhimman abu kafin ya goyi bayan ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel