Atiku ba zai ƙara samun kuri'u Miliyan 11m a 2023 ba, Sanata Kwankwaso
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya kamata Atiku Abubakar ya daina mafarkin samun kuri'u miliyan 11m a 2023
- Tsohon gwamnan na Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa ya ce ko a baya da shi aka taimaka wa Atiku kuma yanzun mutane sun waye
- Ya ce ya shirya tsaf ya karbi ragamar mulkin ƙasar nan kuma ya ceto ta daga matsalolin da suka addabeta
Abuja - Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce Atiku Abubakar ya mance da zancen zai iya samun kuri'u miliyan 11m a 2023.
Kwankwaso ya ce ya kamata ace tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ankara da cewa siyasar Najeriya ta canza salo a shekaru uku da suka gabata, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Jagoran jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙasa ya yi wannan furucin ne ranar Talata a Abuja, jim kaɗan bayan kammala tantance shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Ya ce a halin yanzun yan Najeriya sun shiga taitayin su, sun waye fatan da suke su samu shugaba da zai kawo sauyi a ƙasar nan kuma ya tafiyar da ita kan hanya mai kyau.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dangane da ikirarin ɗan takarar da PDP ta tsayar, Atiku Abubakar, cewa yana da tabbacin kuri'u miliyan 11m a zaben 2023. An jiyo Kwankwaso na cewa:
"A ina daga wurin su wa zai samu kuri'u miliyan 11m? wa ya kawo masa kuri'un? Mu ne nan muka jawo masa su."
"Akwai rabuwar kai da yawa a ƙasar nan kuma idan ba'a ɗauki mataki da wuri ba Najeriya ba zata cigaba ba. Mun ga abinda ya faru a Kano yadda aka karkatar da kuri'u a 2019, haka ba zata faru a 2023 ba."
2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya
"Yan Najeriya na bukatar wanda zai ceto ƙasar su, don haka a 2023 Najeriya zata bukaci wanda ya cancanta, yan Najeriya zasu bi bayan mutanen da zasu iya kuma mu zamu yi aiki da kowa ba tare da duba addini ko kabila ba."
Mu muka taimaka masa a 2019 - Kwankwaso
Kwankwaso wanda ya ce jam'iyyar NNPP ta shiga dukkan gundumomi, kananan hukumomi, jihohi, shiyyoyi da ƙasa, ya ƙara da cewa yana cikin mutanen da suka hana idon su bacci don ganin Atiku ya haɗa kuri'u miliyan 11m a zaɓen 2019.
Tsohon gwamnan ya ce idan yan Najeriya suka zabe shi a shekara mai zuwa, zai magance matsalar tsaro, ya daga darajar ilimi kuma ya haɗa kan kabilu baki ɗaya.
A wani labarin kuma Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023
Ɗan tsohon gwamnan Kwara da Allah ya yi wa rasuwa, Hakeem Lawal, ya lashe zaɓen fidda gwanin SDP na takarar gwamna.
A zaɓen wanda aka canza, Hakeem ya samu kuri'u 606, ya lallasa tsohon shugaban FCC ta ƙasa, Mista Oba, mai kuri'u 177.
Asali: Legit.ng