Da Dumi-Dumi: Zan zaɓi wanda zai gaje ni, ku goya mun baya, Buhari ga gwamnonin APC

Da Dumi-Dumi: Zan zaɓi wanda zai gaje ni, ku goya mun baya, Buhari ga gwamnonin APC

  • Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan gwamnonin APC yayin da yake shirin zaɓar ɗan takarar da yake fatan ya gaje shi a 2023
  • Yayin ganawarsa da gwamnonin kafin tafiyarsa Sufaniya, Buhari ya ce zai duba wasu muhimman abu kafin ya goyi bayan ɗan takara
  • A ranar 6 ga watan Yuni da zai shiga, jam'iyyar APC zata gudanar da zaben fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gaya wa gwamnonin APC cewa zai so ya zaɓi wanda zai gaji kujerarsa kuma yana bukatar goyon bayan su yayin hakan.

Shugaba Buhari ya faɗi haka ne a wurin taronsa da gwamnonin jam'iyyar APC ranar Talata a Aso Villa da ke Abuja, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Buhari da gwamnonin APC.
Da Dumi-Dumi: Zan zaɓi wanda zai gaje ni, ku goya mun baya, Buhari ga gwamnonin APC Hoto: Buhari sallau/facebook
Asali: Facebook

The Nation ta rahoto Buhari ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun sa labule bayan Buhari ya faɗa musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi a 2023

"Domin cigaba da kyawawan tsarukan da jam'iyyar mu ta kafa yayin da muke fuskantar babban taro nan da yan kwanaki, ina bukatar goyon bayan gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki wajen zaɓo magaji na."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wanda zai karɓi tutar jam'iyya a zaɓen 2023 har ya samu nasarar shiga ofishin shugaban ƙasa a tarayyan Najeriya a zaben 2023."

Shugaba Buhari ya faɗa wa gwamnonin cewa, "Akwai tarin bukatar ya samar da jagoranci mai ƙarfi a jam'iyya karkashin wannan lamarin na matakan canza gwamnati."

Buhari ya ce gina shugabanci mai ƙarfin ba wai kawai don ya ƙara inganta sa'ar APC a zaɓe kaɗai bane, har da tabbatar wa jam'iyyar ta zarce kan karagar mulki tun daga sama.

Ta yadda zan zaɓi magaji na - Buhari

A taronsa da gwamnonin, shugaban ƙasan ya faɗa musu abubuwan da zai duba kafin ya zaɓi ɗan takarar da zai goya wa baya daga cikin mutum 25 da ke neman tikitin APC.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

"Abin da zamu sa a gaba shi ne nasarar jam'iyyar mu kuma ɗan takarar da zamu zaɓa wajibi ya kasance wanda zai ba yan Najeriya natsuwar samun nasara da tabbaci tun kafin zaɓe."

A wani labarin na daban kuma Hukumar INEC ta soke amfani da wani muhimmin Fom a zaɓen 2023

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta soke amfani da 'Fom ɗin abun da ya faru' yayin gudanar da zaɓe a faɗin Najeriya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Talata 31 ga watan Maris, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel