Masana'antar Fina Finai Ta Sake Shiga Jimami Bayan Rasuwar Fitaccen Jaruminta

Masana'antar Fina Finai Ta Sake Shiga Jimami Bayan Rasuwar Fitaccen Jaruminta

  • Yayin da ake ci gaba da rasa fitattun jaruman fina-finai, a yau Juma'a an sake sanar da mutuwar wani jarumin a Legas
  • Fitaccen jarumin fina-finan Yarbawa, Ganiyu Oyeyemi wanda aka fi sani da Ogunjimi ya riga mu gidan gaskiya a yau
  • Jarumin fina-finai, Kunle Afod shi ya tabbatar da mutuwar fitaccen jarumin a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu a shafin Instagram

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Masana'antar shirya fina-finan Nollywood ta sake shiga jimami bayan mutuwar fitaccen jaruminta.

An wayi garin yau Juma'a 26 ga watan Afrilu da mutuwar shahararren jarumin fina-finai, Ganiyu Oyeyemi.

Jimami yayin da fitaccen jarumin fina-finai ya kwanta dama
An sake tafka babban rashi yayin da jarumin fina-finan Nollywood, Ogunjimi ya rasu. Hoto: @kunleafod
Asali: Instagram

Yaushe jarumin fina-finan ya rasu?

Kara karanta wannan

Katsina: An shiga makoki bayan 'yan bindiga sun hallaka shugaban APC da wani mutum

Marigayin wanda aka fi sani da Ogunjimi ya rasu ne a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu bayan fama da jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin Nollywood, Kunle Afod shi ya tabbatar da rasuwar marigayin a shafinsa a Instagram a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu.

Afod ya ce tabbas masana'antar shirya fina-finan ta tafka babban rashin fitacce kuma jajaritacce.

"Mun yi iya bakin kokarinmu amma Ubangiji ya fi mu sonka, muna maka fatan samun rahama Baba Ogunjimi."

- Kunle Afod

Shura da fitaccen jarumin fina-finan ya yi

Marigayin ya yi kaurin suna a fina-finan jarumta a bangaren yaren Yarbanci inda da ya fito a manyan fina-finai.

Har ila yau, jarumin kafin rasuwarsa yana yawan fitowa a fina-finan tsafi da kuma maita.

Mace-macen taurarin fina-finai a Najeriya

Wannan na zuwa ne yayin da masana'antar shirya fina-finai ke cikin jimamin rashe-rashen da ta yi a cikin kwanaki.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi yayin da tsohon Sanata ya kwanta dama yana da shekaru 66

Masana'antar ta tafka manyan rashe-rashe na jarumanta da dama tun farkon wannan shekara da muka ciki.

Tsohon sanata ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon sanata a Najeriya, Ayogu Eze ya riga mu gidan gaskiya a birnin Tarayya Abuja.

Marigayin wanda ya wakilci mazabar Enugu ta Arewa daga shekarar 2007 zuwa 2015 ya rasu ne a jiya Alhamis 25 ga watan Afrilu.

Sanatan ya ba da gudunmawa sosai a Majalisar Dattawa inda ya kasance daya daga cikin mambobin kwamitin gyara kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel