Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

  • Gwamnonin da ke mulki a karkashin APC sun yi zama bayan haduwarsu da Muhammadu Buhari
  • Makasudin zaman shi ne a tattauna a kan wanda ya kamata ya yi takarar shugaban kasa a 2023
  • Har zuwa lokacin da aka tashi taron, ba a cin ma matsaya a kan su wanene ya kamata a zaba ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ba a samu matsaya a karshen zaman da gwamnonin jam’iyyar APC suka yi a ranar Talata, 31 ga watan Mayu 2022 domin fitar da ‘dan takara ba.

A wani rahoto da mu ka samu daga Premium Times, mun ji cewa kusan duka gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar sun hadu a birnin Abuja.

Hakan ya biyo bayan Muhammadu Buhari ya zauna da gwamnonin, ya kuma fada masu cewa zai so a ba shi goyon bayan zakulo wanda zai karbi mulki.

Wannan ya sa gwamnonin jihohin suka sa labule dazu domin ajiye magana daya a game da takarar. A karshe dai kan shugabannin bai iya haduwa ba.

Rahoton ya ce an tashi da yammacin yau da nufin za a sake wani zaman da karfe 8:00 na dare.

Majiyar ta shaida cewa wadannan gwamnoni sun gagara cin ma matsaya a kan yadda za a bullowa bukatar da Mai girma shugaban kasa ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin APC
Wasu Gwamnonin APC a Aso Villa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Za a tafi da mutane 2 - Gwamna

Wani gwamna ya ce abokan aikinsa sun amince a zakulo sunayen mutane biyu a kai gaban shugaban kasa. Za a dauki Gwamnan Kudu da na Arewa.

“Mun yi imani shugaban kasa bai da wani ‘dan takara da yake ransa. Shiyasa gwamnoni suka mu ka bukatar su mika sunayen takwarorinmu biyu.”
“Za a dauki gwamna daya daga Arewa, gwamna daya daga Kudu domin shugaban kasa ya zaba.”

- Wani Gwamna na APC

A kai takara zuwa Kudu

A taron, wasu gwamnonin jihohi sun nuna zai yi wahala a samu ‘dan siyasar Kudu da zai iya doke Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP ta tsaida domin ya yi takara.

Don haka aka fara bijiro da maganar a maida hankali wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa daga Arewa a APC, wannan batu ya fusata Gwamnonin Kudu.

Me Buhari ya fadawa Gwamnoni?

Ku na da labari cewa da yake magana da gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja, Muhammadu Buhari ya nemi a maida hankali kan yadda siyasa ta ke canzawa.

Shugaban na Najeriya ya nemi hadin kan gwamnonin da ke mulki, ya ce dole ne kansu ya hadu wajen fito da wanda zai rikewa APC tuta a zaben shekara mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel