An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

  • Wani mutum ya gamu da ajalinsa a mashayar giya bayan wani ya buga masa kwalban giya a kai bayan rikici ya shiga tsakaninsu
  • Wata majiya ta ce wanda ake zargi da kisan ya yi yunkurin ture mamacin ne da motarsa shi kuma ya masa fada nan take suka fara cacan baki
  • Rundunar yan sandan Jihar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar mutumin ta kuma kama wanda ake zargin tana mai cewa za a zurfafa bincike

Bayelsa - Wani mutum mai matsakaicin shekaru da ba a riga an gano sunansa ba ya mutu a wani mashayar giya dake Jemeni Street, Abakaliki, Babban Birnin Jihar Ebonyi.

Wani majiya da ta yi magana da Jaridar Leadership amma ta nemi a sakaya sunanta tace lamarin da ya faru misalin karfe 7 na yamma ya tada hankulan mutane a unguwar.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa
An fasa wa wani kai da kwalban giya a mashaya ya mutu. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan yan sandan Jihar Ebonyi, Aliyu Garba ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mutanen biyu da suka yi rikicin a buge suke.

"Lamarin ya faru kuma wanda abin ya faru da shi ya mutu. Mutanen biyu - wanda aka kashe da wanda ya yi kisar tare suka taho.
"Tabbas, ya kamata ka san cewa a buge suke. Kawai sun samu karamin rashin jituwa ne a mashayar, dayansu ya dauki kwalba ya buga wa dayan a kansa. Abin ya faru tsakanin su biyu ne.
"An garzaya da wanda aka buga wa kwalban a kai zuwa asibiti amma daga baya ya rasu.
"A yanzu, na tabbatar jami'an mu sun kama wanda ake zargin. Ina fatan za su iya baka karin bayani daga baya."

Dalilin afkuwar rikicin tsakanin mutanen biyu

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

Majiyar ta ce rikicin ya samo asali ne lokacin da wanda ake zargin mai suna Ayoola, mai sayar da abinci a kasuwar Ekeaba, ya yi yunkurin bige marigayin da motarsa hakan yasa marigayin ya nemi sanin dalili.

Ya ce:

"Mutane sun saba taruwa a wurin su ci abinci su sha abin sha. A ranar marigayin yana shigowa sai wanda ake zargin ya shigo da mota a sukwane ya kusa bige shi.
"Marigayin ya fusata ya tambaye shi dalili, wanda ake zargin ya daga murya yana masa barazana. Bisa alamu akwai rikici tsakaninsu ko kuma sun bugu.
"Mutane sun yi kokarin basu hakuri amma ya cigaba da yi wa marigayin barazana, kawai sai wanda ake zargin ya dauki kwalba ya buga masa a kai shi kuma ya fadi a kasa.
"Bayan yan mintuna, sai aka gano ya dena motsi jini na fitowa daga bakinsa da hanci. Mutane da dama suka tsere."

Kara karanta wannan

Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni

Majiyar ta kara da cewa bayan afkuwar lamarin, yan sanda sun taho sun kama wanda ake zargin sun kuma dauke gawar mammacin.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoto, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ya Yi Digiri a Jami'ar Harvard Ta Birtaniya Ya Bayyana Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

Asali: Legit.ng

Online view pixel