2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini

2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini

  • Wani limamin cocin Christ Apostolic Church (CAC), Fasto Alamu David, ya ce jagoran APC, Bola Tinubu ne zai gaje Buhari a 2023
  • Fasto David ya bayyana cewa Allah ya nuna masa Tinubu a matsayin wanda zai lashe babban zaben kasar mai zuwa
  • Ya kuma yi kira ga yan kudu maso yamma da jiga-jigan APC da su marawa tsohon gwamnan na Lagas baya don ya cika alkawarin Allah

Lagas - Fasto Alamu David na cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Abule Egba, jihar Lagas, ya yi ikirarin cewa mai neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ne zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Malamin addinin, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa Allah ya nuna masa a ranar 24 ga watan Yunin 2008 cewa wani mutum mai suna Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

Fasto Davida ya kuma bayyana cewa ya yi imani cewa lokacin da Tinubu zai cika wannan alkawarin na Ubangiji ya yi, jaridar The Nation ta rahoto.

2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini
2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Saboda haka, malamin ya yi kira ga al’ummar yankin kudu maso yammacin kasar da jiga-jigan jam’iyyar APC da su marawa Tinubu baya domin wannan al’amari da aka nuna masa ya tabbata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bukaci Yarbawa da su lura cewa “Asiwaju danmu ne kuma ubanmu ne, ya kamata mu duba bayansa sannan mu kalle shi a matsayin dan takara daya tilo da ya shirya dawo da yancinmu da muka rasa a 2023.”

Fasto David ya ce:

“Asiwaju ne mai ceto na lokacinmu kuma hana shi damar zai yi daidai da mummunan lamarin da ya faru da Baba MKO Abiola da Baba Awolowo wanda musamman mu Yarbawa muke danasanin abun daga baya.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki Rochas Okorocha, an tantance shi a matsayin ‘Dan takara kafin a rufe kofa

“Kada a bari tarihi ya maimaita kansa domin illar abun zai zarce tunani.
“Na yi imani da cewa mutum kamar Baba Bola Ahmed Tinubu ne kadai ya dace da wannan kujera. Ya kasance dan siyasa ne mai kyawawan manufofi.
“Shi kadai ne dan takarar APC, jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a wancan lokacin wanda ya zama gwamna a kudu maso yamma. Ya yiwa jihar Lagas manyan tsare-tsare wanda ke nan har rana mai kamar ta yau.
"Haka kuma, kyawawan dabarunsa ya kasance tsani ga yan siyasa da dama da suka dare kujerun shugabanci. Imma kujerun gwamna, minista ko na sanata.
"Shugaban kasa mai ci da mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai, duk sun hau wannan tsani don samun kujerunsu.
"Lokaci ya yi da za a marawa kura aniyarta ta hanyar marawa kudirinsa baya. Ina kuma rokon dattawan kabilar Yarbawa da su shiga lamarin da mara masa baya."

Kara karanta wannan

Yadda ta kaya da Tinubu ya bayyana gaban kwamitin tantance masu neman takara a APC

2023: Malaman musulunci sun ce lallai Bayarabe Musulmi suke so ya gaji Buhari

A wani labarin, wata gamayyar kungiyar malaman musulunci Yarbawa a Najeriya (CYMSN) ta bayyana cewa lallai Bayarabe Musulmi ne zai zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.

Kungiyar ta kuma koka kan yunkurin tauye hakkin Musulman kudu da kuma hana su damar yin takarar manyan mukamai na shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a kasar nan, jaridar Leadership ta rahoto.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, mukaddashin shugaban kungiyar, Sheikh AbduRasheed Mayaleke, ya bayyana cewa za su nuna turjiya a duk wani yunkuri na mayar da Musulman Yarbawa baya idan aka zo batun shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel