Ana zargin Gwamna Wike da dumbuzar Naira Biliyan 30 a harin zama ‘Dan takaran PDP
- Dr. Dakuku Peterside ya taya Atiku Abubukar murna a kan samun takarar shugaban kasa a PDP
- Tsohon ‘dan majalisar na Ribas ya ce Nyesom Wike ya kashe N30bn, duk da haka bai yi nasara ba
- Peterside ya ba Wike shawara ya ajiye gadarar da yake ji da ita, ya bi Alhaji Atiku Abubakar a PDP
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Dakuku Peterside ya fito yana zargin Nyesom Wike da yi wa gwamnatin jihar Ribas asarar Naira biliyan 30 a neman takarar shugaban kasa.
PM News ta ce Dr. Dakuku Peterside ya jefi Gwamna Nyesom Wike da wannan zargi ne a jawabin da ya fitar na taya Atiku Abubakar murnar samun takara.
Fitaccen ‘dan siyasar na jihar Ribas ya ce Nyesom Wike ya kashe Naira biliyan 30 a wajen neman zama ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya.
A karshe Wike ya sha kashi a hannun tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.
Wike kifin rijiya ne - Dakuku
Dakuku Peterside ya ce sakamakon zaben tsaida gwanin ya nuna Gwamna Wike ba kowa ba ne a siyasar kasa, domin tasirinsa bai wuce a jihar Ribas ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An rahoto tsohon shugaban hukumar ta NIMASA yana cewa duk da Wike ya kashe Naira biliyan 30, masu tsaida ‘dan takara a PDP ba za su zabe shi ba.
Wike ya yi wa Atiku biyayya
Peterside wanda jigo ne a APC, bai iya bada wata hujja da ta nuna Gwamnan na Ribas ya kashe wadanan makudan kudi kuma daga cikin baitul malin Ribas.
Har ila yau, a jawabin na sa, ‘dan siyasar ya ba Gwamnan na sa shawarar ya bi Atiku Abubakar wanda ya lashe tikitin PDP domin ya samu karin kwarewa.
Peterside ya kara yin ikirarin Wike ya na facaka da kudin al’umma, ya gaza biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkinsu saboda burinsa na zama shugaban kasa.
“Wike ya nuna bai da kwarewa da zurfin da ake bukata wajen yin takara a siyasar kasa.”
“Ina kira ga Wike ya dawo gida, ya cire girman kansa, kuma ya sallama kansa ga Atiku, ya koyi yadda ake siyasar kasa da yadda ake bugawa.”
Siyasar APC a 2023
A gefe guda kuwa labari na zuwa cewa Gwamnoni za su mikawa Shugaban Najeriya sunayen abokan aikinsu, daga nan sai ya zabi wanda yake so ya gaje shi.
Watakila Gwamnonin APC za su dauki gwamna daya daga Arewa, sai daya daga Kudu, a kai gaban Mai girma Muhammadu Buhari wanda ke da wuka da nama.
Asali: Legit.ng