An sake maka Atiku Abubakar a kotu, ana neman haramta masa tsayawa takara har abada

An sake maka Atiku Abubakar a kotu, ana neman haramta masa tsayawa takara har abada

  • Johnmary Jideobi ya je kotu a Abuja, ya shigar da kara a kan Atiku Abubakar, PDP da kuma INEC
  • Lauyan ya nemi Alkali ya hana jam’iyyar PDP tsaida Atiku Abubakar takara a duk wani zaben Najeriya
  • Jideobi ya na ikirarin Atiku ba cikakken ‘dan Najeriya ba ne, don haka bai cancanta da mukami ba

Abuja - Wani Lauya da ke aiki a Abuja, Johnmary Jideobi, ya roki babban kotun tarayya ta haramtawa Atiku Abubakar neman kujerar shugaban kasa.

Premium Times ta ce Johnmary Jideobi yana kalubalantar zama ‘dan kasar Atiku Abubakar wanda ya yi shekaru takwas yana mataimakin shugaban kasa.

A karar da ya shigar a kotun da ke zama a garin Abuja, Jideobi ya hada da Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP, hukumar INEC da babban lauyan gwamnati.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Shehu Sani ya shawarci Atiku kan irin wanda ya kamata ya zaba a matsayin mataimaki

Lauyan ya hakikance a kan cewa a dokar kasa, Atiku bai cancanta ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ba, domin ba a Najeriya aka haife sa ba.

A cewar Lauyan, Atiku Abubakar ya zama ‘dan Najeriya ne a 1961, lokacin da wasu bangaren kasar Kamaru suka shigo Najeriya bayan an samu ‘yancin-kai.

PDP za ta saba doka a 2023

Mai karan ya ce kyale wanda ake tuhuma (Atiku Abubakar) ya shiga zaben 2023 a matsayin ‘dan takara, yana nufin jam’iyyar PDP ta sabawa dokokin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar
Wazirin Adamawa Atiku Abubakar Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Hakan zai ci karo da sashe na 1(1) & (2), 25 da 131(a) na kundin tsarin mulkin 1999 a cewar Lauyan.

Har ila yau, Lauyan ya ce a doka, nauyi yana kan hukumar INEC na ganin cewa ba ta bar wani wanda ba mutumin Najeriya ba ya samu iko da gwamnatin kasar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Vanguard ta ce Jideobi ya nemi kotu ta yarda cewa jam’iyyar PDP ba ta da ‘dan takarar shugaban kasa.

Lauyan ya kuma roki gwamnati ta bada umarnin da zai hana Atiku Abubakar rike kujerar shugaban kasa ko wani mukami a gwamnati har karshen rayuwarsa.

Rahoton ya ce har zuwa yanzu ba a sa ranar da za a saurari wannan shari’a a gaban kotu ba. A baya an yi irin wannan shari'a, kuma Wazirin Adamawa ya yi nasara.

Atiku yana neman mataimaki

A farkon makon nan, mun kawo maku rahoto cewa Atiku Abubakar ya na neman wanda zai dauko a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya a 2023.

Daga cikin zabin akwai Udom Emmanuel wanda ya yi takara da Atiku wajen samun tikitin jam’iyyar PDP, sai kuma Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel