Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

  • Mohammed Hayatu-Deen, dan takarar zama shugaban kasa na PDP, ya janye daga tseren neman tikitin jam'iyyar
  • Hayatu-Deen ya bayyana janyewarsa daga takarar ne a wata wasika da ya aike wa Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa
  • Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmawa da goyon baya wajen ganin PDP ta samu nasara a babban zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mohammed Hayatu-Deen, daya daga cikin manyan yan takarar da ke neman tikitin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya janye daga tseren.

Tsohon Manajan-Darakta na rusasshen bankin FSB, ya sanar da janyewarsa daga tseren ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, Daily Trust ta rahoto.

Shahararren dan kasuwar ya janye daga tseren ne yan kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya janye daga takarar sannan ya fice daga jam’iyyar ta PDP.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren
Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren Hoto: Mohammed Hayatu-Deen Support group
Asali: Facebook

Sai dai kuma, Hayatu-Deen ya yi alkawarin ci gaba da kasance a babbar jam’iyyar adawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Na kasance mai bin diddigin siyasar Najeriya tsawon shekaru masu yawa, amma ban taba samun damar shiga siyasar saboda yadda nake kula da manyan cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu da sauransu.
“Cike da damuwa da tarin bakin ciki, na lura da tabarbarewar dukkanin al’amuran rayuwar kasarmu – wanda ke da alaka da karuwar talauci, rashin kau da kai na addini, fashi da makami, garkuwa da mutane, satar mai, cin hanci da rashawa, satar arzikin kasa, rikicin kabilanci da addini da kuma rugujewar ayyuka da cibiyoyin gwamnati.
“Na yi shirin tabbatar da ganin cewa an cimma abubuwan ci gaban Najeriya a yayin shugabancinmu. Mun shirya mayar da Najeriya ta zama cibiyar tattalin arziki wanda zai tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga mafi akasarin 'yan kasarmu.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

“Na so samar da zaman lafiya ta hanyar kawo karshen ta’addanci kowani iri wanda ke faruwa sakamakon rashin cikakken tsari mai inganci da rashin kulla alaka da wadanda abin ya shafa da kuma inganta hukumar leken asirinmu, rundunar sojoji da na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
“Na so kawo karshen yawan kulle jami’o’inmu da sauran makarantun gwamnati saboda yajin aiki. Yanzu haka sa muke magana, wani rukuni na yajin aiki na gudana kuma babu wanda ya san yaushe za a bude jami’o’inmu.
“Saboda wadannan ne na shiga harkar siyasa don samar da mafita masu dorewa ga wadannan matsalolin.
“Na kasance cike da kishi da jajircewa wajen ganin na ceto kasarmu da ke gab da durkushewa.
“Aiki da na yi a gida da waje da kuma gudunmawar da nake baiwa tattalin arzikin kasar da na siyasa ya sa na dauki aniyar tunkarar kalubaken da kasarmu ke fuskanta da kuma karfin gwiwar shiga wannan shiri wanda yawancin shugabanninmu suka yi watsi da shi. Abun takaici tsarin siyasar ya zama mai ban tsoro, rashawa da son zuciya.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

“A tsawon watanni uku da suka gabata na samu damar zantawa da yan Najeriya daga bangare daban-daban na rayuwa. Wannan yasa na yanke shawarar cewa dole a hidimtawa Najeriya, idan bah aka ba makomarmu za ta halaka.
“Na shiga tseren a matsayin dan damokradiyya, da budaddiyar zuciyar yin takara da yarda da sakamakon tsarin zabe na gaskiya da adalci."

Yayin da ya ke bayyana dalilansa na janye takarar, Hayatu-Deen ya ce abu ne da ya shafi "harkar kui ce karara”.

Sai dai kuma ya yi alkawarin cewa zai bada gudunmawa da goyon bayan sosai wajen ganin PDP ta samu nasara a babban zaɓen 2023, rahoton Premium Times.

Dan siyasar ya ci gaba da cewa:

“A karshe, a matsayina na amintaccen dan jam’iyya kuma mai bin tsarin dimokuradiyya, zan ci gaba da shiga harkokin jam’iyya da ni da dumbin magoya bayana a kowane lokaci don ganin nasarar babbar jam’iyyarmu.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

A gefe guda, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kira wani taron gaggawa na shugabanninta na kasa a kokarinta na duba batutuwan gaggawa da suka taso, ciki har da yiwuwar sake dage babban taronta na kasa da aka shirya yi a yau.

Ana sanya ran taron na kwamitin NWC wanda ke gudana yanzu haka a Abuja zai magance lamuran da suka shafi shawarar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yanke na tsawaita wa'adin kammala zaben fidda gwani na jam'iyyu a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel