Shugaban kungiyar Malamai ya doke Sanata wajen zama ‘Dan takarar Gwamna a APC

Shugaban kungiyar Malamai ya doke Sanata wajen zama ‘Dan takarar Gwamna a APC

  • Shugaban kungiyar NUT, Nasiru Idris APC ta tsaida a matsayin ‘dan takarar Gwamnan jihar Kebbi
  • Kwamred Nasiru Idris zai rikewa jam’iyyar APC mai mulki tuta a zaben 2023, zai gwabza da PDP
  • Idris ya doke Sanata Yahaya Abdullahi wanda suke rigima da bangaren Gwamna Atiku Bagudu a APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Shugaban kungiyar NUT ta malaman makaranta, Nasiru Idris, ya zama ‘dan takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam’iyyar APC.

Jaridar The Cable ta ce Nasiru Idris ya doke Sanata Yahaya Abdullahi da Abubakar Gari-Malam wajen samun tikitin APC mai mulki na jihar Kebbi.

A halin yanzu, Sanatan Yahaya Abdullahi shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu, 2022 Idris Yahuza ya bada sanarwar sakamakon zaben tsaida gwanin, ya ce Abdullahi bai samu kuri’a ko daya ba.

A cewar malamin zaben, Malam Nasiru Idris ya samu kuri’u 1, 055 a cikin 1, 090 da aka kada, shi kuma Malam Gari-Malam ya tashi da ragowar kuri’u 35.

Nasiru Idris ya yi murna

Rahoton da ya fito daga hukumar dillacin labarai na kasa ya tabbatar da cewa Idris ya yi farin cikin samun nasarar zama ‘dan takarar gwamnan APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar Malamai
Nasiru Idris da Gwamna Atiku Bagudu Hoto: @kbstgovt
Asali: Facebook

Idris ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC mai mulki da suka iya gudanar da zaben fitar da ‘dan takarar ba tare da an samu wata rigima ba.

Haka zalika ‘dan takarar gwamnan ya jinjinawa ‘ya ‘yan jam’iyyar da suka kada kuri’a a zaben.

The Cable ta ce baya ga zamansa shugaban kungiyar NUT na kasa, Idris shi ne mataimakin shugaban kungiyar kwadago watau NLC na Najeriya.

Malami ya halarci zaben

Wadanda suka halarci zaben tsaida gwanin sun hada da Mai girma gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN.

Ana tunani Gwamna Bagudu ne ya marawa Idris baya wajen samun tikiti. Sanata Abdullahi kuma yana tare da bangaren tsohon Gwamna, Adamu Aleiro.

Idris Ajimobi ya samu takara

Ku na da labari cewa Idris Abiola-Ajimobi ya zama ‘dan takarar APC na shiyyar Kudu maso yammacin Ibadan II bayan sauran 'yan takara sun janye masa.

Mai dakinsa, Fatima Ganduje za ta yi murna biyu, domin yayanta, Umar Abdullahi Ganduje ne wanda APC ta ke so ya canji Tijjani Jobe a majalisar tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel