‘Dan tsohon Gwamnan da ya rasu, Surukin Ganduje ya lashe zaben takarar ‘Dan Majalisa

‘Dan tsohon Gwamnan da ya rasu, Surukin Ganduje ya lashe zaben takarar ‘Dan Majalisa

  • Idris Abiola-Ajimobi ne ya zama ‘dan takarar APC na shiyyar Kudu maso yammacin Ibadan II
  • Mai gidan Fatima Ganduje ya samu tikiti ne bayan sauran ‘yan takaran APC sun janye masa
  • Fatima Ganduje za ta yi murna biyu, Umar Abdullahi Ganduje ake so ya canji Tijjani Jobe a Kano

Oyo - Idris Abiola-Ajimobi, wanda ‘da ne a wajen Marigayi Abiola Ajimobi shi ne ‘dan takarar jam’iyyar APC a mazabar Kudu maso yammacin Ibadan.

Premium Times ta ce Idris Abiola-Ajimobi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da jam’iyyar APC ta shirya na kujerar ‘yan majalisu a ranar Alhamis.

Idris Ajimobi zai rikewa APC tuta a yankin Kudu maso yammacin Ibadan a zabe mai zuwa.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto cewa ‘yan takarar wannan kujera ta majalisar dokoki sun janye, sun ba Ajimobi damar takara.

Kara karanta wannan

LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

Abiola-Ajimobi ya godewa Ubangiji da ya samu wannan dama, da kuma abokan hamayyarsa da suka sallama masa, tare da magoya baya da suka dafa masa.

Ajimobi ya sha alwashin zai yi abin da jam’iyyar APC za ta yi alfahari da shi idan ya je majalisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Surukin Ganduje ranar aure
Fatima Ganduje tare da Mai gida da Mahaifinta Hoto: BBCnewsHausa
Asali: Facebook

Rahoton ya tabbatar da cewa matashin ya yi alkawari zai samar da wakilci mai kyau a yankin Ibadan, tare da sa ran zai doke duk sauran jam’iyyu a 2023.

“Duk ina yi mana fatan alheri a zaben 2023. Allah ya sa mu yi tsawon rai domin mu ci daga guminmu.”

Idan za a tuna mahaifinsa, Abiola Ajimobi ya rasu ne bayan an nada shi a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar kudancin Najeriya.

Ajimobi ya rasu a lokacin annobar COVID-19 kafin ya fara aiki a ofis. Kafin nan ya yi shekaru takwas a jere yana mulki a jihar Oyo a karkashin APC.

Kara karanta wannan

‘Dan takara ya fasa rabawa ‘Ya ‘yan PDP Naira Miliyan 92 tun da sun ki zaben shi

A gefe guda kuma, Umar Abdullahi Ganduje ya zama ‘dan takarar jam’iyyar APC a mazabar tarayya na yankin Rimin Gado/Dawakin Tofa da Tofa.

Injiniya Umar Ganduje ‘danuwa ne a wajen Fatima Ganduje-Ajimobi wanda ta ke auren Ajimobi. Fatima Ganduje ta na cikin hadiman shugaban majalisa.

'Ya 'yan manya sun samu takara

Ku na da labari cewa yaron Ambasada Aminu Wali, Sadiq Wali ya zama ‘dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Kano na tsagin su Sanata Bello Hayatu Gwarzo.

Su kuma bangaren Shehu Wada Sagagi sun tsaida Mohammed Abacha a matsayin ‘dan takararsu. Mahaifinsa ya yi tsawon shekaru biyar yana mulkin soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel