Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

  • Nura Dankadai, tsohon kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Kano ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa
  • Dankadai ya sanar da ficewarsa ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban APC na mazabarsa ta Tsohon Gari a karamar hukumar Tudun Wada
  • Tun a watan Afrilu ne ya yi murabus daga mukaminsa don ya mayar da hankali kan takarar da zai yi na kujerar majalisa ta Tudun Wada/Doguwa

Jihar Kano - Tsohon kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafi, Nura Dankadai ya fita daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a kasa.

Daily Trust ta rahoto cewa ya sanar da hakan ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban APC na mazabar Tsohon Gari a karamar hukumar Tudun Wada a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC
Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga APC. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Dankadai da wasu kwamishinoni sun yi murabus daga kujerunsu a watan Afrilu domin su fuskanci takarar da za su yi a 2023 bisa umurnin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya nuna sha'awar yin takarar kujerar majalisa na wakilcin mazabun Tudun Wada/Doguwa na Kano.

Duk da cewa bai sanar da jam'iyyar da za shiga a gaba ba, ana yada jita-jitar cewa zai iya koma wa jam'iyyar New Peoples Party, NNPP, wacce tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ke yi wa jagora.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel