Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

  • Zubairu Hamza Massu, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya fita daga jam'iyyar All Progressives Party, APC
  • Massu ya ce ya fita daga jam'iyyar ne saboda rikice-rikicen da aka yi a jam'iyyar a baya-bayan nan da kuma rashin yi wa yankinsa ta Kano ta Kudu adalci
  • Ana hasashen cewa Hamza Massu zai bi sahun wasu yan siyasan Jihar Kano da suka fice daga APC a baya-bayan nan suka koma Jam'iyyar NNPP

Jihar Kano - Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP
Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Koma NNPP. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Abin da yasa Massu ya fita daga APC

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

"Bayan abubuwan da suke faruwa a jam'iyyar a baya-bayan nan da kuma tuntubar mutanen mazaba ta da magoya baya da masu ruwa da tsaki a Sumaila da Kano ta Kudu, na rubuta wannan don sanar da kai cewa na yi murabus daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
"Na yanke shawarar hakan ne saboda rashin adalci, rashin demokradiyya ta cikin gida da rashin kulawa da ake yi wa Kano ta Kudu," ya ce a cikin wasikar.

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

A bangare guda, Tsohon kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafi, Nura Dankadai ya fita daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Daily Trust ta rahoto cewa ya sanar da hakan ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban APC na mazabar Tsohon Gari a karamar hukumar Tudun Wada a Kano.

Dankadai da wasu kwamishinoni sun yi murabus daga kujerunsu a watan Afrilu domin su fuskanci takarar da za su yi a 2023 bisa umurnin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya nuna sha'awar yin takarar kujerar majalisa na wakilcin mazabun Tudun Wada/Doguwa na Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel