Kano: SSG Ɗin Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Sun Koma NNPP

Kano: SSG Ɗin Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Sun Koma NNPP

  • Guguwar sauya sheka ta sake diban wasu manyan yan siyasan Kano daga jam'iyyar All Progressives APC ta sauke su a jam'iyyar NNPP (Mai Kayan Marmari) ta Kwankwaso
  • Cikin wadanda suka koma NNPP din akwai Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Ali Makoda; Shugaban karamar hukumar Danbatta, Audu Wango; Murtala Kore, Dan Majalisar Jihar Kano da wasu fitattun yan siyasan
  • Ana sa ran shima tsohon gwamnan Kano kuma Sanata na Kano Central, Malam Ibrahim Shekarau yana hanyarsa ta koma wa NNPP

Jihar Kano - Shugaban ma'aikatar fadar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, Ali Makoda, ya jagoranci wasu fitattun yan siyasa sun fice daga jam'iyyar APC sun koma jam'iyyar NNPP.

Da ya ke magana da Daily Nigerian a daren ranar Juma'a, Mista Makoda ya tabbatar da komawarsa zuwa jam'iyyar New Nigeria People's Party ta Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugabannin Ƙananan Hukumomi 2 Da Auditan APC Sun Koma NNPP
Kano: SSG Na Ganduje, Shugabannin Ƙananan Hukumomi 2 Da Auditan APC Sun Koma NNPP. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ya riga ya mika takardun murabus dinsa a matsayin shugaban ma'aikatan fada ga Ganduje a yau din.

An tarbi Mista Makoda tare da sauran wadanda suka fice daga APC a gidan Kwankwaso da ke Miller Road kamr yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Wasu cikin yan siyasan da suka koma jam'iyyar ta NNPP a ranar Juma'a

Cikin wadanda suka fice daga APC zuwa NNPP akwai Badamasi Aliyu, dan majalisar tarayya mai wakiltan Ɗanbatta/Makoda; Murtala Kore, dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Ɗanbatta da; Abdullahi Wango, shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta.

Saura sun hada da Ahmed Speaker, Audita na APC ta Jihar Kano; Najib Abdussalam, shugaban matasan APC na yankin; Umar Maitaidau, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Makoda; Haliru Danga Maigari, tsohon dan majalisar jiha mai wakiltar Rimingado/Tofa da; Hafizu Sani Maidaji, tsohon dan majalisar jiha mai wakiltar Ɗanbatta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Har wa yau, cikin wadanda suka koma NNPP din akwai Safiyanu Harbau, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Tsanyawa/Kunchi, Habiba Yandalla, tsohuwar shugaban mata da wasu fitattun yan siyasan.

Idan za a iya tunawa a ranar 6 ga watan Mayu, yan majalisar dokokin jihar Kano su 9 sun fice daga PDP sun koma NNPP.

A kuma ranar Juma'an, Abdulmumin Jibrin, mai yi wa Tinubu yakin neman zaben takarar shugabancin kasa ya fice daga APC ya koma NNPP tare da tsohon Kwamishinan Kasafi, Nura Dankadai.

Ana kyautata zaton Sanata Ibrahim Shekarau shima zai koma NNPP

An sa ran tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata na Kano Central shima zai sanar da komawarsa NNPP a hukumance a karshen mako.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Gwamna Ganduje ya ziyarci gidan Ibrahim Shekarau a daren ranar Juma'a da nufin ya shawo kansa game da batun ficewarsa daga APC amma ba a san tabbacin yada ganawarsu ta kasance ba kawo yanzu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel