Buhari Ya Umurci Su Amaechi, Malami, Ngige Da Akpabio Su Yi Murabus Cikin Kwana 5

Buhari Ya Umurci Su Amaechi, Malami, Ngige Da Akpabio Su Yi Murabus Cikin Kwana 5

  • Daga karshe Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke da niyyar takara a zaben 2023 su ajiye aikinsu
  • Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu ne ya sanar da hakan bayan taron FEC da Shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba
  • Mohammed ya ce Shugaba Buhari ya bawa ministocin wa'adin kwana biyar daga yau su mika murabus dinsu wato kafin ko ranar 16 ga watan Mayu

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022, Channels Television ta rahoto.

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Umurci Ministocinsa Su Yi Murabus Cikin Kwana 5
Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Umurci Dukkan Ministocinsa Da Ke Son Takara Su Yi Murabus. Hoto: Channels Television.
Asali: Twitter

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari'a), Godswill Akpabio (Neja Delta).

Shima hadimin shugaban kasa Tolu Ogunlesi ya tabbatar da umurnin na shugaban kasa ga ministoci masu son yin takara kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce:

"Yanzun nan: Dukkan ministocin fadar Shugaba Buhari da ke son yin takara za su yi murabus kafin ko ranar 16 ga watan Mayun 2022."

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel