2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

  • Shugabannin Kungiyar Fulani da ke Abuja su na kokarin ganin Goodluck Ebele Jonathan ya koma fadar shugaban kasa
  • Wani sabon rahoto ya nuna yadda tsohon shugaban kasar ya samu haduwa da su a ranar Talata, 10 ga watan Mayu akan kin amincewarsa da fom din takarar da aka siya masa
  • Majiyoyi da dama sun nuna yadda Jonathan ya ce ya sauya ra’ayi kuma zai sanar da su labari mai dadi dangane da bukatar tasu

Abuja - An yi taron tsakar dare da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da shugabannin Kungiyar Fulani da ke Abuja wadanda su ka siya masa fom din takarar shugaban kasa na N100m don su tattauna su ji matsayarsa akan tsayawa takarar.

Vanguard ta ruwaito cewa yayin taron da kungiyar masu mara wa Jonathan baya a ranar Talata, 10 ga watan Mayu, ya nuna rashin jin dadinsa akan siya masa fom din takarar ba tare da an neman izininsa ba, laifin da su ka amince kuma su ka bayar da hakuri akai.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar
Zaben 2023: Jonathan ya sauya ra’ayi akan tikitin APC, da alamu zai yi takarar. (Photo: Goodluck Ebele Jonathan)
Asali: Twitter

Dr. Ibrahim Abdullahi, shugaban kungiyar Fulanin ne ya bayar da hakurin.

A bangarensu, makiyayan sun bayyana cewa sun yi hakan ne don nuna jin dadinsu akan yadda ya yi amfani da Naira Biliyan 60 don bunkasa ilimin Almajirai a lokacin yana mulki da kuma samar da ci gaba a fannoni daban-daban.

Majiyoyin da su ka halarci taron sun sanar da Vanguard cewa bayan sauraron matsayar makiyayan, tsohon shugaban kasar ya amince da bukatarsu ta tsayawa takara.

Kuma ya ce za su ji labari mai dadi nan ba da jimawa ba, duk da dai bai sanar da lokacin da za su ji daga gare shi ba.

Yanzu haka akwai ‘yan gani-kashenin Jonathan da a baya su ka nuna rashin amincewarsu da komawarsa jam’iyya mai mulki, amma a yanzu sun sauya ra’ayi.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Cikin kwanakin nan wasu magoya bayansa su ka koma mara wa Fulanin baya akan cewa ya kamata Jonathan ya cikasa fom din takarar don gudun wuce ranar da ofishin jam’iyyar ta Abuja ta shimfida.

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Ina mai tabbatar maka da cewa magoya bayan Jonathan su na ta mara masa baya akan ya tsaya takarar. Hakan ya sa wasunsu su ke ta taimaka masa wurin cikashe fom din.”

Jonathan ya bar PDP ya koma APC, inji hadimin Shugaba Buhari

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fannin labarai, Bashir Ahmad, ya ce Jonathan ya bar jam’iyyar adawa ta PDP inda ya koma APC.

Ahmad ya bayyana hakan ne ta wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter wacce Legit.ng ta gani a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu.

Kamar yadda ya rubuta:

“Yanzu, Goodluck Jonathan ya bar jam’iyyar adawa ta PDP, ya dawo jam’iyyar mu ta APC.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel