Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi watsi da tsarin yar tinke, zaben deleget za'a yi, Kano ta fi yawan deleget

Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi watsi da tsarin yar tinke, zaben deleget za'a yi, Kano ta fi yawan deleget

  • Jam'iyyar APC ta yi watsi tsarin yar tinke da ittifaki, zaben deleget za'a yi don fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
  • Yayinda jihar Kano tafi kowa yawan deleget da adadin mutum 465, Abuja ke da mafi karanci mutum 56
  • Legit ta tattaro muku adadin deleget da kowace jiha ke da shi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023 sabanin yadda tayi a zaben 2019.

Jam'iyyar ta yanke shawarar amfani da deleget wajen zaben wanda zai wakilci jam'iyyar a zaben shugaban kasa.

An yanke shawarar haka ne a taron Majalisar zartaswa NEC ta 11 da ke gudana a Transcorp Hotel dak birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas

Kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya bada zabi uku na yadda za'a gudanar da zaben fidda gwani.

Ittifaki, yar tinke wanda aka fi sani da kato bayan kato, da kuma na deleget.

Jam'iyyar APC na da Deleget 7,800.

Yaynda jihar Kano tafi yawan deleget, Abuja ke da mafi karanci..

NEC Jam'iyyar APC
Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi watsi tsarin yar tinke, zaben deleget za'a yi Hoto: @APCNigeria
Asali: Facebook

Legit ta tattaro muku adadin deleget da kowace jiha ke da shi:

Kano: 465

Katsina: 384

Borno: 324

Osun: 308

Lagos: 304

Oyo: 292

Jigawa: 266

Niger: 251

Ogun: 248

Nasarawa: 245

Abia: 154

Adamawa: 184

Akwa Ibom: 165

Anambra: 163

Bauchi: 202

Bayelsa: 79

BenueL: 180

Cross River: 194

Kara karanta wannan

2023: Deleget na Jihohi 10 da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwanin APC

Delta: 170

Ebonyi: 154

Edo: 168

Ekiti: 216

Enugu: 131

Gombe: 134

Imo: 236

Kaduna: 234

Kebbi 213

Kogi: 222

Kwara: 195

Ondo: 200

Plateau: 185

Rivers: 151

Sokoto: 193

Taraba: 146

Yobe: 222

Zamfara: 169

FCT: 53

APC ta sanar da ranar gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa

Majalisar zartaswa NEC ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta amince da ranar 30 da 31 ga Mayu matsayin ranakun gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Wannan na cikin sanarwar Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barista Felix Morka, bayan taron majalisar NEC da ya gudana a Abuja ranar Laraba.

Barista Morka yace kuma ranar 18 Mayu za'a gudanar da zaben fidda gwanin gwamnoni,

Asali: Legit.ng

Online view pixel