Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

  • Ana kyautata zaton nan ba da dadewa ba Farfesa Yemi Osinbajo zai sanar da Duniya zai yi takara
  • Yemi Osinbajo ya yi zama da Gwamnonin APC, ya shaida masu zai nemi tikitin jam’iyya a zaben 2023
  • Mataimakin shugaban Najeriyan zai ayyana takararsa ba tare da ya kira wani taro na musamman ba

AbujaRahotanni na nuna cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai sanar da Duniya niyyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a yau Litinin, 11 ga watan Afrilu 2022.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto da ya tabbatar da cewa Mai girma mataimakin shugaban kasa zai nemi ya gwabza da tsohon mai gidansa, Bola Tinubu.

Tun ba yau Farfesa Yemi Osinbajo ya fara wannan shirye-shirye ba, amma sai a karshen makon da ya gabata zuwa yanzu ne abubuwa suke kara bayyana a fili.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin takara a zaben shugaban kasa na 2023 ba tare da an yi wani taro ko kiran wata gayya ba.

Muddin abubuwa ba za su canza zani ba, bidiyo ne kurum ake tunani Farfesa Osinbajo zai fitar mai tsawon mintuna bakwai zuwa goma ga al’ummar Najeriya.

A wannan bidiyo da za a saki, mataimakin shugaban kasar zai tabbatarwa ‘yan Najeriya burinsa na ganin ya gaji mai gidansa, Mai girma Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban kasa
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: @laoluakandeofficial
Asali: Facebook

Maganar takara ta yi nisa

Da zarar Osinbajo ya fito da wannan faifen bidiyo, jaridar ta ce za a shiga yada shi a kafafen sada zumunta na zamani, sai masu yi masu yakin zabe su shiga aiki.

Tuni dai Osinbajo ya bude ofishin yakin neman zabe a layin Buchanan Crescent da ke unguwar Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja domin ya cin ma nufinsa.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Osinbajo ya kawo sabon salo

Wannan ya sabawa yadda aka ga sauran masu neman takarar shugaban kasa musamman a APC su ke yi. Babu wanda ya bayyana burin takara da faifen bidiyo.

Bola Tinubu wanda shi ya fara bude kofa a farkon shekarar nan, ya ayyana niyyarsa ne gaban ‘yan jarida bayan ya yi wani zama na musamman da shugaban kasa.

Haka zalika Rochas Okorocha ya tara jama’a ne ya sanar da su cewa ya na neman shugabanci. Abin da aka ga Hon. Rotimi Amaechi ya yi kenan a ranar Asabar.

Osinbajo ya zauna da gwamnoni

An samu labari cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tara duk gwamnonin APC domin sanar da su cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Farfesa Osinbajo ya shirya bikin buda baki, ya bayyana masu aniyarsa ta gaje shugaban kasa Buhari. Kafin nan, an ce ya sanar da kowane gwamna kafin su hadu.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Osinbajo v Tinubu dsr

Maganar ta ba mutane mamaki, inda aka ji wasu su na cewa ba su yi tunanin haka za ta faru ba.

Malam Abdulhaleem Ringim ya ce

"Wannan karon ban cinka daidai ba, ban taba tunani Osinbajo zai yi takara yayin da Tinubu ya ke neman mulki ba. Mulki bala'i ne."

Sulaiman Yaro ya na cewa:

"Watakila ya na tare da Tinubu ne. Amma har yanzu ina shakkar cewa Osinbajo zai yi takara tare da Jagaban.""

Asali: Legit.ng

Online view pixel