Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023

Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023

  • Hukumar INEC ta kara tuna wa jam'iyyun siyasa jadawalin sharuɗɗan da ta kafa da abun da ka iya biyo baya a zaɓen 2023
  • INEC ta gargaɗi jam'iyyu a kan bin dukkan tanade-tanaden doka da demokaraɗiyya wajen fitar da yan takara
  • A cewar hukumar ba zata yi wata-wata ba wajen watsi da yan takara matuƙar ba'a bi hanyoyin da ta gindaya ba

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ƙara ankarar da jam'iyyun siyasa kan jadawalin sharuɗɗan da ya zama wajibi su bi kafin babban zaɓen 2023.

INEC tace duk jam'iyyar da ta saɓa wa kundin dokokin zaɓe 2022, ba zata karɓi ɗan takarar da ta gabatar a zaɓe mai zuwa ba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan mutane, Festus Okoye, ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar INEC.
Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tun a ranar 26 ga watan Fabrairu, hukumar ta fitar da jadawalin gudanar da ayyukan zaɓen 2023, wanda ya haɗa da zaɓen fidda gwani na jam'iyyu da kuma mika mata yan takara.

Sharuɗɗan da INEC ta kafa wa jam'iyyun siyasa

Sanarwan ta ce:

"Hukuma na ƙara jaddada wa jam'iyyu cewa wajibi ne su yi bi demokaradiyyar cikin gida sau ɗa ƙafa, tun daga kwansutushin ɗin su, tsari, kundin zaɓe, da sauran dokoki da sharuɗɗan da INEC ta kafa."
"Tilas jam'iyyu su gudanar da sahihi, karɓaɓen zaɓen fidda gwani a mazaɓu 1,491 da za'a shirya babban zaɓen 2023, wanda ya dace da sashi na 29 da na 84 na kundin zaɓe 2022."

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Ɗan takarar dake mafarkin gaje Buhari a 2023 zai maka PDP a Kotu kan tsadar Fam

"Duk jam'iyyar da ta ƙi bin waɗan nan dokokin wajen zaɓenta na fitar da yan takara, ba zamu saka ɗan takararta da wannan lamarin ya shafa ba a kowane muƙami ne."

Shin suna bin waɗan nan sharuɗɗa?

Okoye ya ƙara da bayanin cewa dukkan waɗan nan ayyuka na kan layi ɗaya da kundin mulkin Najeriya 1999 da aka gyara da kuma kundin zaɓen 2022.

"Zuwa yanzu biyu cikin 14 na yadda INEC ta tsara a jadawalinta sun kammalu. Abu na gaba shi ne zaɓen fidda gwani, wanda hukuma ta ware wa kwana 61 (4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yuni 2022)"

Bugu da ƙari, Okoye ya ce doka ta tanadi cewa tilas INEC ta sa ido wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani na kowace jam'iyya, kamar yadda The Cable ta rahoto

Ya kuma gargaɗi jam'iyyu kan gaza sanar da INEC duk wani taro ko gangami da suka shirya don fitar da ɗan takara na kowane Ofishin siyasa, kamar yadda doka ta tanada zata soke taron.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa na amince na jagoranci yakin neman zaɓen Yahaya Bello ya gaji Buhari, Hafsat

A wani labarin Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari

Shugaban matasan APC reshen yan Najeriya mazauna Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa, ya koma NNPP.

Dakta Usman Shehu, ya ce tsohuwar jam'iyyarsa ta gaza cika wa yan Najeriya alƙawurran da ta ɗauka a yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel