2023: Dalilan da suka sa na karɓi ragamar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Yahaya Bello, Hafsat Abiola

2023: Dalilan da suka sa na karɓi ragamar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Yahaya Bello, Hafsat Abiola

  • Ɗiyar fitaccen ɗan siyasan nan da ake ganin ya lashe zaɓen 12 ga Yuni, 1993, MKO Abiola, ta karbi ragamar tallata Yahaya Bello
  • Hafsat Abiola ta ce ba'a jan hankalinta da kuɗi, akwai abubuwa da yawa na nagarta da ta gani a jikin gwamna Bello
  • A hasashen Hafsat, Bello ne kaɗai zai iya kai Najeriya gaci da zaran yan Najeriya sun amince da shi a 2023

Lagos - Darakta Janar ta kungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasan gwamna Yahaya Bello na Kogi, Hafsat Abiola, ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sanya ta karɓi muƙamin.

Ɗiyar Chief MKO Abiola, wanda ake ganin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga watan Yuni, 1993, ta ce bayan ta yi nazari kan Bello, ta gano cewa yana da ƙwarewar da zai kai Najeriya ga gaci.

Kara karanta wannan

Wata mata ta bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, tace Allah ya faɗa mata zata gaji Buhari

Hafsat tace ɗaya daga cikin kamanceceniyar siyasa tsakanin mahaifinta da Gwamna Bello, shi ne kin yarda da Uban Gida a siyasa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Hafsat Abiola
2023: Dalilan da suka sa na karɓi ragamar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Yahaya Bello, Hafsat Abiola Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta ƙara da cewa hakan ya jawo wa gwamna tsana da "Zalunci," da ya sha fama da su a abubuwa da ɗama da suka shafi gwanatinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin Bello zai iya samun tikitin APC?

DG Hafsat, wacce ta yi jawabi a wata hira da Arise TV ranar Lahadi, ta nuna kwarin guiwarta cewa Bello zai karɓi tutar takara a APC duk da shugaban jam'iyya ya fito daga yankinsa.

Vanguard ta rahoto Ta ce:

"Wajibi a bar yan Najeriya su zaɓi mutanen da suke so, wannan shi ne ma'anar demokaraɗiyya. Mahaifina bai nemi takara don kare martabar yankinsa ba, ya maida hankalinsa kan Najeriya ne kaɗai."

Kara karanta wannan

An samu ƙari: Gwamnan Arewa zai bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

DG ɗin ta ce wata kamanceceniyar ita ce marigayi Abiola ya yi amanna da dunƙulewar Najeriya kamar Yahaya Bello, inda ta bayyana cewa yana girmama kowa ba tare da duba kabilar da ya fito ba.

"Irin haka na hanga a Yahaya Bello, ya fito takara, ba tare da damuwa da ƙaramar ƙalbilar da ya hito ba, kuma ya ci nasara, yanzu kuma ya sake fitowa. Haka mahifina ya yi, lokacin ana ganin Bayerabe ba zai iya ba."
"Yahaya Bello shi ya dace ya jagoranci Najeriya, kuɗi ba su ruɗa ta, ina yin abun da zuciyata ta yarda da shi ne. A makonni 7 masu zuwa, zamu yi aiki tuƙuru kuma idan muka samu nasara, za mu ba mara ɗa kunya."

A ranar Asabar 2 ga watan Afrilu. 2022, Gwamna Yahaya Bello, ya sanar da kudirin shiga takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC.

A wani labarin na daban kuma Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a PDP

Kwamishinan muhalli da albarkatun karkashin ƙasa na Enugu ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Mista Edeoga, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel