'Yar MKO Abiola Ta Yi Wa 'Yar Uwarta Kaca-Kaca Saboda Kwatanta Mahaifinsu Da Yahaya Bello

'Yar MKO Abiola Ta Yi Wa 'Yar Uwarta Kaca-Kaca Saboda Kwatanta Mahaifinsu Da Yahaya Bello

  • Tundun Abiola, lauya kuma mai gabatar da shirye-shirye ta yi wa 'yar uwarta Hafsat Abiola kaca-kaca saboda amfani da sunan mahaifinsu wurin kamfen
  • Tundun ta nuna bacin ranta matuka saboda kwatanta MKO Abiola da Hafsat ta yi da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi
  • Ta gargadi Hafsat din, ta mayar da hankali wurin tallata, mai gidanta Yahaya Bello da ayyukansa ba kwatanta shi da Abiola ba wacce ta ce halinsu ba daya bane

Tundun Abiola, fitacciyar mai gabatar da shirye-shirye a Arise TV, ta soki yar uwarta, Hafsat Abiola-Costello saboda kwatanta Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi da marigayin mahaifinsu, rahoton Daily Trust.

Hafsat Abiola, wacce ita ce shugaban kungiyar yakin neman zaben shugabancin kasa na Bello, ta kwatanta taken takararsa na 'Hope23' da na Abiola, wanda ake dauka matsayin wanda ya lashe zaben June 12, 1993 wato 'Hope'93'.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

'Yar MKO Abiola Ta Yi Wa 'Yar Uwanta Kaca-Kaca Saboda Kwatanta Mahaifinsu Da Yahaya Bello
Ki dena amfani da sunan mahaifinmu, ki mayar da hankali wurin tallata ayyukan mai gidanki: Yar Abiola ta fada wa yar uwanta. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

An yi hira da ita a Arise TV a ranar Lahadi inda ta yi bayanin dalilin da yasa ta amince ta jagoranci yakin neman zaben Bello, tana mai cewa halayen gwamnan sun yi kama da na mahaifinta.

Ta ce marigayi MKO Abiola ya yi imani da kasa Najeriya guda, kamar Bello, tana mai cewa baya nuna banbanci tsakanin talaka da mai kudi.

"Akwai wasu halaye da na gani tare da Gwamna Bello. Ya fito takara duk da cewa ya fito ne daga kabila mara girma a Kogi kuma ya yi nasara, kuma ya sake fitowa. Mahaifi na shima haka ya yi, a lokacin da aka yi imanin cewa Bayerabe ba zai iya zama shugaban kasa ba," a cewarta a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

Tudun ta nuna damuwarta kan wannan tsokacin da 'yar uwarta ta yi

Amma, Tudun ta nuna damuwa kan kalaman 'yar uwarta, tana mai bukatar ta ta kyalle mahaifinsu a wannan batun ta mayar da hankali wurin tallata manufofin mai gidanta.

Daily Trust ta rahoto cewa Tudun, wacce lauya ec kuma mai gabatar da shirye-shirye, yar Mrs Bisi Abiola ce, matar MKO ta uku, yayin da Hafsat yar Kudirat ce, matar Abiola ta biyu wacce aka kashe yayin gwagwarmayar June 12.

Tudun, wacce ke cike da mamaki lokacin da ta ke magana a Arise TV tare da abokin gabatarwarta, Reuben Abati, ta ce ta ji takaicin abin da yar uwarta ta furta yayin hirar da aka yi da ita.

Ta ce,

"Ina jure wasu abubuwa daga gare ta, amma duk da cewa ban yi mamaki ba, hakan baya nufin bai dace ba.
"Ina magana ne kan yar uwata, Hafsat, wacce ita ce DG na yakin neman zaben Yahaya Bello, da kwatanta shi da ta yi da mahaifi na. Akwai yan siyasa da dama a tawagarsa amma duk cikinsu babu wanda ya yarda ya wulakanta mahaifinsa saboda mai gidansa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa na amince na jagoranci yakin neman zaɓen Yahaya Bello ya gaji Buhari, Hafsat

"Ki fito ki yi magana game da mai gidanki, abin da ya yi a baya da abin da ya ke fatan yi wa Najeriya amma kada ki saka mahaifinmu a batun. Ba ta da ikon yin hakan, ba sunanta bane, sunan mu ne. Sunan yayan mu da za mu haifa a gaba ne kuma ya kamata su yi alfahari da sunan. An azabtar da mahaifi na a cewa UN, kadaici azabatarwa ne a cewarta. An azabtar da shi sannan aka halaka shi amma kawai sai a rika bata masa suna.
"Kuma wani mutum a shirin da ke yi wa wani kamfen shima ya yi amfani da sunan mahaifi na domin cimma burinsa na siyasa kuma abin ya bata min rai. Kowa ya dena ambaton sunansa, abin ya fi bata min rai duba da cewa ba su da wata kamanceceniya."

2023: Yahaya Bello Ya Yi Alƙawarin Mayar Da Ƴan Najeriya Miliyan 20 Attajirai Idan Aka Zaɓe Shi Shugaban Ƙasa

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

A bangare guda, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ta bayyana wa kowa shirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, The Cables ta rahoto.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a Eagles Square da ke Abuja inda ya ce zai dada daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya, ta hanyar mayar da ‘yan Najeriya miliyan 20 miloniyoyi zuwa shekarar 2030.

Asali: Legit.ng

Online view pixel