Jerin yan takarar shugaban kasa 13 na PDP da suka siya fom din takara yayin da jam'iyyar ta tara N486m

Jerin yan takarar shugaban kasa 13 na PDP da suka siya fom din takara yayin da jam'iyyar ta tara N486m

A kalla yan takarar shugaban kasa 13 ne suka siya fom din takara na jam’iyyar PDP zuwa yanzu gabannin babban zaben 2023.

Adadin ya kai 13 ne bayan gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, shahararren dan kasuwa, Muhammad Hayatudden, sun mallaki nasu fom din takarar a ranar Laraba, 30 ga watan Maris.

Sannan kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, shima ya yanki nasa fom din a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris.

Jerin yan takarar shugaban kasa 13 na PDP da suka siya fom din takara yayin da aka tara N486m
Jerin yan takarar shugaban kasa 13 na PDP da suka siya fom din takara yayin da aka tara N486m Hioto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Ga cikakken jerin sunayen wadanda suka yanki fom din takarar shugabancin kasar:

1. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da Abdullahi Adamu, sabon shugaban APC

2. Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki

3. Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Anyim Pius Anyim

4. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed

5. Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal

6. Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike

7. Mawallafin Mujallar Ovation International, Dele Momodu

8. Oliver Diana Teriela

9. Nwachukwu Anakwenze

10. Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

11. Dan kasuwa, Muhammad Hayatudeen

12. Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi

13. Wanda ya kafa kuma tsohon shugaban kamfanin Neimeth Pharmaceutical, Sam Ohuabunwa

Yawan kudin da PDP ta tara daga sayar da fom din takarar

Jam’iyyar PDP ta dora fam din takararta da na nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa kan naira miliyan 40.

An kuma tattaro cewa Oliver Teriela Diana, wacce ita kadai ce mace a cikin yan takarar shugaban kasar, ta biya naira miliyan 6 don mallakar dukka fom din biyu.

Kara karanta wannan

Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

Da yawan yan takarar da suka siya fom din, PDP ta tara naira miliyan 486 daga siyar da fom din.

2023: Atiku, Tambuwal da sauran jiga-jigan PDP sun gana don gina yarjejeniya kan dan takarar shugaban kasa

A baya mun ji cewa, manyan yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun sake ganawa don tatauna ra’ayinsu yayin da ake ci gaba da muhawara kan yankin da jam’iyyar za ta baiwa tikiti gabannin babban zaben 2023.

Har yanzu dai babbar jam’iyyar adawar kasar bata bayyana yankin da za ta baiwa tikitinta na takarar kujerar ta daya ba, yayin da yan takara ke ci gaba da zawarcin kujerar.

Yayin da yan siyasar kudu ke kokarin ganin an mika tikitin zuwa yankinsu, takwarorinsu na arewa ma na so a mallakawa yankinsu tikitin, lamarin da ka iya kawo sauyi a al’adar jam’iyyar na yin karba-karba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan takaran kujeran shugaban APC 6 sun janyewa wanda Buhari ya zaba, Abdullahi Adamu

Asali: Legit.ng

Online view pixel