Gwamnan Arewa zai ayyana shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

Gwamnan Arewa zai ayyana shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

  • Gwamnan jihar Kogi dake arewa ta tsakiya, Yahaya Bello, zai sanar da shiga takarar shugaban ƙasa a hukumance ranar Asabar
  • Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin shirye-shirye na yaƙin neman zaɓensa ne ya bayyana haka a Lokoja, ranar Alhamis
  • A baya dai, gwamna Bello ya ce zai sanar da kudirinsa ne bayan babban taron APC na ƙasa, wanda aka kammala

Kogi - Alamu sun bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zai ayyana kudurinsa na neman takarar shugaban ƙasa a hukumance, ranar Asabar 2 ga watan Afrilu, 2022 a Filin Eagle Square.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin shirye-shirye na yaƙin neman zaɓen gwamna, shi ne ya bayyana haka ga jaridar Daily Trust a Lokoja, ranar Alhamis.

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Gwamnan Arewa zai ayyana shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa gwamna Bello zai sanar da burinsa na neman ɗora wa daga inda shugaba Buhari zai tsaya ranar Asabar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Gwamnan Bello na jam'iyyar APC ya samu kiraye-kiraye da nuna goyon baya daga dukkan sassan ƙasar nan na ya fito takarar kujera Lamba ɗaya.

Matasa da mata sune suka fi bukatar ya fito takara, wanda a cewarsa sun matsa masa da rokon ya nemi ofishin shugaban ƙasa a zaben 2023.

Wannan ya yi dai-dai da maganarsa a baya, inda ya bayyana cewa zai amsa kiran masoyansa bayan kammala babban taron APC na ƙasa.

A lokacin, Yahaya Bello, ya ce ya maida hankali ne kan shirye-shiryen taron, da kuma ganin jam'iyya ta samu nasarar gudanar da shi.

Gwamnan Kogi na ɗaya daga cikin gwamnonin APC dake hankoron samun tikitin takara karkashin jam'iyya mai mulki.

Jagoran APC na ƙasa kuma tsohon gwamna Legas, Bola Tinubu, shi ma yana cikin masu neman APC ta ba su tutar takara.

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

A wani labarin kuma Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar APC

Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Gombe, Abubakar Sadiq Ibrahim Kurba, ya yi murabus daga APC.

Ƙurba, wanda takwarorinsa mambobin majalisa suka tsige a 2020, ya ce ya ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel