Yadda Jam'iyyar APC zata cigaba da mulkin Najeriya a 2023, Sanata Adamu

Yadda Jam'iyyar APC zata cigaba da mulkin Najeriya a 2023, Sanata Adamu

  • Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sha alwashin kawo wa jam'iyya nasara a babban zaɓen 2023
  • A cewarsa aikin jam'iyya ba na mutum ɗaya bane, wajibi kowa ne mamba a kwamitin NWC da masu ruwa da tsaki su tashi tsaye
  • Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya yi wannan magana ne bayan karban ragama daga hannun Mala Buni

Abuja - Sabon shugaban APC da aka rantsar, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce kwamitin ayyuka NWC ƙarƙashin kulawarsa zai yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar APC a 2023.

Adamu ya yi wannan jawabin ne a Sakatariya ta ƙasa ranar Laraba, yayin karɓan ragamar APC daga hannun Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya.

Daily Trust ta rahoto sabon shugaban na cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ba zai lamurci shan kaye ba a zaɓen.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari a ayyana shiga tseren kujerar gwamna a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba

Sanata Adamu da Gwamna Buni
Yadda Jam'iyyar APC zata cigaba da mulkin Najeriya a 2023, Sanata Adamu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan Nasarawan yace lashe zaɓen 2023 ba ƙaramin abu bane dole sai an shirya masa, bisa haka ya roki sauran mambobin NWC da masu ruwa da tsaki na APC su yi aiki da kishi har mafarkin jam'iyya ya tabbata.

A kalamansa ya ce:

"Ta wace hanya zamu lashe babban zaɓe? mutane na ta cece-kuce APC ba ta da tabbas ɗin ɗan takara. Zamu tara girma, da gaskiya, ayyuka a zo a gani da shugaba Buhari zai bari a kan tikitin mu."
"Zamu yi aiki dare da rana, ƙasa da watanni 12 nan gaba zamu dumfari babban zaɓe, ɗan haka kowa ya tashi tsaye. Ɗan abun da na sani game da shugaban ƙasa shi ne ba su ga maciji da rashin nasara."
"Saboda haka ba zancen faɗuwa a APC daga yau, zamu yi aiki domin nasara a tare. Idan ɗayanku dake tare da ni, kar ku ɓoye komai, duk abinda ya taso ku faɗa mun."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya ayyana shiga tseren takara a zaɓen 2023

Yadda APC zata cigaba da mulki a 2023

Adamu ya ƙara da cewa wajibi kowane mamba tun daga sama har ƙasa su haɗa kai domin mutum ɗaya ba ya ɗaukar jinka.

"Dole mu zama masu biyayya, mu zama masu murya ɗaya tawaga ɗaya, idan muka rarrabu, mu magance lamarin nan take. Ƙasar mu ta zarce ɗai-ɗaikun mu, kazalika jam'iyya ta fi kowane mamba."

A wani labarin kuma mun kawo muku yadda Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa

Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya kammala aikinsa ya mika ragamar tafiyar da APC hannun sabon shugaba

Sanata Abdullahi Adamu, ya karɓi jagorancin APC a Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel