Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar APC

  • Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Gombe, Abubakar Sadiq Ibrahim Kurba, ya yi murabus daga APC
  • Ƙurba, wanda takwarorinsa mambobin majalisa suka tsige a 2020, ya ce ya ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansa
  • Ya kuma shaida wa manema labarai a wata tattaunawa cewa zai faɗi dalilansa bayan ya karbi katin mamba na sabuwar jam'iyyarsa

Gombe - Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe wanda ya sauka ba da jimawa ba, Abubakar Sadiq Ibrahim Kurba, ya yi murabus daga kasancewa mamban APC ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kurba ya sanar da matakinsa ne a wata wasika da ya sanya wa Adireshin kakakin majalisa na yanzu ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Daga APC zuwa SDP: Ana neman mai maye gurbin dan majalisar Kwara bayan ya sauya sheka

Zauren majalisar dokoki ta jihar Gombe.
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A wasiƙar da ya aike wa majalisar, Honorabul Kurba, ya ɗauki matakin murabus bisa wasu dalilai da ya barwa kansa sani kuma nan take.

Kurba ya zama shugaban majalisar dokokin ne bayan an rantsar da majalisa ta shida a watan Yuni na shekarar 2019.

Sai dai a watan Nuwamba, 2020 abokanan aikinsa mambobin majalisa suka tsige shi bisa hujjar cewa yana haɗa baki da ɓangaren zartarwa kan ayyukan ɓangaren masu doka.

Bayan haka kuma Kurba ya samu saɓani da gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe bayan dangantakar gwamnan da Sanata Danjuma Goje ta yi tsami.

An yi amannar cewa tsohon kakakin ɗan a mutun Sanata Goje ne, kuma alamu sun nuna yana tsagin Sanatan tun bayan rasa kujerarsa a Majalisa.

Wace jam'iyya zai koma?

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a PDP

A wata tattaunawa ta wayar Salula, Ƙurba ya bayyana cewa zai sanar da motsinsa na gaba a siyasa nan gaba kaɗan ba da jimawa ba.

Yace:

"Duk lokacin da na karbi katin zama mamba na sabuwar jam'iyyar da na koma, zan faɗa wa mutanen Gombe dalilin da yasa na yi murabus daga APC."

A wani labarin kuma PDP ta samu gagarumin koma baya a Osun, Ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

Tsohon ɗan takarar gwamna kuma babban jigo a jam'iyyar hamayya PDP reshen Osun, Dr Akin Ogunbiyi, ya tsame kansa daga cikin jam'iyyar.

Mista Ogunbiyi, ya sanar da matakin da ya ɗauka na barin PDP a wata wasikar murabus da ya aike wa shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel