Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

  • Majalisar wakilai ta Najeriya ta dauki dumi game da batun kashe-kashen 'yan Najeriya a kwanakin nan
  • Shugaban masu rinjaye a majalisar ya yi kira ga a bar 'yan Najeriya su mallaki makamai domin kare kai
  • Hakazalika, wasu 'yan majalisun sun bayyana bacin ransu ga yadda jami'an tsaro ke halin ko in kula ga lamarin tsaro

Abuja - Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa, ya ce ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu duba da tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Dan majalisar wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta Kano ya bayyana haka ne a zaman da majalisar ta yi a yau Alhamis a lokacin da ake muhawara kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasan fasinja a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

Dan majalisa ya damu da yadda ake kashe 'yan Najeriya ba gaira ba dalili
Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Doguwa, wanda wannan mummunan al’amari ya kai shi zub da hawaye, yana kan ra’ayin cewa jami’an tsaro sun gaza, don haka bai kamata ‘yan kasa su ci gaba da zama cikin cutarwar ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi ba.

Wasu 'yan ta'adda na tasowa daga Kano

Wani dan majalisa, Honorabul Aminu Suleiman wanda kuma dan jam’iyyar APC ne a nasa gudunmawar ya ce hukumomin tsaro na nuna halin ko in kula da lamarin tsaro, Channels Tv ta ruwaito.

Ya ja hankalin majalisar kan wasu samari a jihar Kano da ake kira Suka, wanda ya ce suna tasowa kuma za su iya zama wata barazana ta tsaro.

Suleiman ya nuna shakku kan tasirin majalisar dangane da kudurorin da aka zartar kan harkokin tsaro, ya kuma bukaci ‘yan majalisar da su shiga yajin aikin har sai an shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Kana ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na babban kwamandan tsaron kasar da ya yi aiki da alhakin da ya rataya a wuyansa da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

Ra'ayoyin sauran 'yan majalisu

‘Yan majalisar sun kuma nuna shakku kan aikin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, wanda ke rike da mukamin tun 2015 ba tare da yin ko gizau ba.

Honorabul Ahmed Jaha a lokacin da yake bayar da gudunmuwarsa ya yi magana a fusace, inda ya koka kan yadda wani dan majalisar ya rubuta wasikar yabo ga daya daga cikin shugabannin tsaro wanda yace hakan ya bata masa rai.

Jaha, wanda ke wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza, ya ce zai yi maganin dan majalisar daga karshe.

Daga karshe dai shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya yi nasarar sanya shi ya janye maganar.

Honorabul Dachung Bagos ya bukaci majalisar ta dakatar da sake kudi ga jami’an tsaro har sai sun yi lissafin duk kudaden da aka sake garesu zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Tinubu Ya Nemi a Tara Wa Iyalan Waɗanda Suka Jikkata Kuɗi

Domin karrama wadanda suka mutu a makon da ya gabata sakamakon harin na ‘yan bindiga, ‘yan majalisar sun yi addu’o’i na musamman tare da dage zaman majalisar.

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

A labari makamancin wannan, tsohon dan majalisar dokokin kasar wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya magantu a kan lamarin rashin tsaro.

Shehu Sani ya ce duba ga yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar, ya kamata a bari yan Najeriya su dunga daukar makamai domin kare kansu a hukumance.

Legit Hausa ta rahoto yadda yan bindiga suka kai harin bam a kan jirgin kasan da ke hanyar zuwa Kaduna daga Abuja dauke da fasinjoji a daren ranar Litinin.

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

A wani labari, ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya bukaci yan Najeriya da su kawo gudunmawar kudi domin kula da wadanda harin jirgin kasa na ranar Litinin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da yan bindiga suka far ma jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Amaechi, wanda ya ziyarci wajen harin a ranar Talata, ya ce ba don an toshe sayan manyan kamarori da na’urori na layin dogo da kudinsu ya kai naira biliyan 3 ba, da an dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel