Da ɗuminsa: Babu gwamnati da ta taɓa rayuwar ƴan Najeriya kamar ta Buhari, Adamu

Da ɗuminsa: Babu gwamnati da ta taɓa rayuwar ƴan Najeriya kamar ta Buhari, Adamu

  • Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya tabbatar da cewa babu gwamnati da ta taba rayuwar ƴan Najeriya kamar ta Buhari
  • Sanata Adamu ya zayyano ire-iren ayyukan inganta rayuwa kamar titunan mota, layikan jiragen kasa da sauran ayyuka da gwamnati ta yi
  • Ya mika godiyarsa ga shugabanni, gwamnoni, ƴan jamiyya da suka dauka amana suka basu kuma ya yi fatan su sauke ta yadda ya dace

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da za ta kai gwamnatin Buhari taba rayukan yan Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Adamu ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko a matsayin shugaban jam’iyya mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Da ɗuminsa: Babu gwamnati da ta taɓa rayuwar ƴan Najeriya kamar ta Buhari, Adamu
Da ɗuminsa: Babu gwamnati da ta taɓa rayuwar ƴan Najeriya kamar ta Buhari, Adamu. Hoto daga @Governormasari
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito yadda Adamu ya bayyana shugaban jamiyya mai mulki a taron da aka yi a dandalin Eagle Square, Abuja, ranar Asabar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a nasa jawabin, shugaban jam'iyyar mai mulki ya mika gayyatar abokantaka ga 'yan takarar da suka janye, yana mai cewa "zasu yi nasara a lokacin da Allah ya nufa".

“A madadin takwarorina, sabbin zababbun mambobin kwamitin ayyuka na kasa na babbar jam’iyyarmu ta APC, ina mika godiyarmu ga Allah Madaukakin Sarki, godiya ta tabbata ga shugabanmu, shugaban kasan Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, Gwamnonin Jam'iyyarmu, Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Musamman da Kwamitin Tsare-tsare na Kasa (CECPC), wakilan taron, ga dukkan shugabanninmu a matakai daban-daban , da kuma dukkan ‘ya’yan babbar jam’iyyarmu ta kasa baki daya da suka zabe mu a wadannan mukamai masu matukar daraja.”

Kara karanta wannan

Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan

“Mun amince da babban nauyi da kuka dora a wuyanmu kuma za mu yi aiki tukuru don ganin mun cika burin ku don ci gaban babbar jam’iyyarmu da kuma kasarmu.
“Kusan shekaru bakwai kenan gwamnatocin jam’iyyar APC a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suke ta fama ba dare ba rana domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar manufofi da tsare-tsare da ayyuka daban-daban.
“Babu wata gwamnati a tarihin Najeriya da ta taka rawar gani wajen gina muhimman ababen more rayuwa da kuma inganta rayuwar al’ummar Najeriya kamar mulkin shugaba Buhari. Ayyukan da a da suka wanzu kawai a cikin mafarkin ’yan Najeriya kamar gadar Neja ta Biyu, kammala gyaran titi daga Legas zuwa Ibadan, titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan, titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna, bututun Ajaokuta-Kaduna-Kano da dai sauransu.
“Wasu da dama, ko dai an fara su ne kuma aka kammala su a lokacin mulkin mu ko kuma an gadar da su a halin da aka yi watsi da su kuma sun samu ci gaba cikin sauri a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Kara karanta wannan

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

“Babu wata gwamnati da za ta gamsar da kowa, duk yadda ta yi aiki tukuru. A koyaushe za a bar wasu ayyukan kuma kowane aikin da aka yi zai ci gaba da buƙatar kulawa, faɗaɗawa da haɓakawa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel