Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki

Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki

  • Shugabancin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa Atiku Abubakar zai kasance cikin tattaunawar da ake yi don cimma matsaya daya wajen fitar da dan takara
  • Saraki ya bayyana hakan yayin da yake watsi da ikirarin cewa an tsame tsohon mataimakin shugaban kasar a yarjejeniyar
  • Sai dai kuma, Saraki ya bayyana cewa har yanzu ana kan tattaunawa kan batun fitar da dan takarar shugaban kasa, inda ya ce za a yi taro nag aba a jihar Sokoto

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi watsi da hasashen da wasu ke yin a cewa an mayar da Atiku Abubakar saniyar ware wajen tattauna batun tsayar da dan takarar shugaban kasa daya na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Vanguard ta rahoto cewa Saraki ya gana da Gwamna Bala Muhammed da Gwamna Aminu Tambuwal, wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP kamar shi a kwanan nan, da nufin cimma matsaya wajen fitar da dan takarar yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki
Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi kan ko sun yi ganawar ne da nufin yiwa Atiku taron dangi, Saraki ya ce wadanda ke ikirarin suna son haddasa rabuwar kai ne a tsakanin mambobin jam’iyyar.

Saraki ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wadanda ke irin wadannan hasashen makirai ne wadanda basa taba ganin alkhairin abu. Ba mu tsame kowa ba. Kamar yadda muka fadi, za mu je mu shi kansa Atikun.
“Za mu je mu ga sauran masu takara. Akwai sauran masu takara a jam’iyyar. Wannan ba batun tsame wani bane. Game da hada kan kowa ne da ra’ayin kasar nan. Kuma za ku gani idan muka fara kewayawa, amma ba mu takaita kowa ba.”

Rahoton ya kuma kawo cewa Saraki ya bayyana cewa za a ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar fitar da dan takarar shugaban kasa na yarjejeniya, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

“Za a yi taro na gaba ne a Sokoto. Wanda gwamnan na Sokoto zai sama mai masaukin baki. Muna son sanar da ku cewa mun yi tattaunawa masu kyau.
“Yadda muke ci gaba da ganawa, haka za mu ci gaba da bayyana ra’ayoyinmu game da muhimmancin hadin kan jam’iyyarmu, saboda mun yarda cewa PDP ce kadai za ta taimaka mana wajen fita daga matsalolin da muke ciki a yau.”

‘Yan Arewa sun yi watsi da su Atiku da Saraki, su na goyon bayan mulki ya koma yankin Kudu

A gefe guda, gamayyar kungiyoyi masu cin gashin kansu 45 daga jihohin Arewacin Najeriya da Abuja sun nuna rashin goyon bayan yankin ya cigaba da mulki.

Jaridar Punch ta ce wadannan kungiyoyin su na goyon bayan mulki ya koma kudancin kasar nan.

‘Yan tafiyar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria sun bayyana cewa za su yi adawa ga duk ‘dan takarar da aka tsaida daga Arewa.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel