‘Yan Arewa sun yi watsi da su Atiku da Saraki, su na goyon bayan mulki ya koma yankin Kudu

‘Yan Arewa sun yi watsi da su Atiku da Saraki, su na goyon bayan mulki ya koma yankin Kudu

  • Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria ta kira taron manema labarai a garin Kaduna
  • Matsayar kungiyar Arewa Concerned Civil Society Organization shi ne mulkin Najeriya ya bar Arewa
  • Abdulsalam Mohammed-Kazeem yana ganin zai yi kyau shugaban kasa ya fito daga Kudu a 2023

Kaduna - Gamayyar kungiyoyi masu cin gashin kansu 45 daga jihohin Arewacin Najeriya da Abuja sun nuna rashin goyon bayan yankin ya cigaba da mulki.

Jaridar Punch ta ce wadannan kungiyoyin su na goyon bayan mulki ya koma kudancin kasar nan.

‘Yan tafiyar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria sun bayyana cewa za su yi adawa ga duk ‘dan takarar da aka tsaida daga Arewa.

A cewar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria, idan za ayi adalci da zaman lafiya, daga kudu ya dace a samu magajin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

Mai magana da yawun bakin kungiyar, Abdulsalam Mohammed-Kazeem ya fitar da jawabin matsayar da suka cin ma a wajen taron manema labarai.

Ganin zabe ya karaso, Abdulsalam Mohammed-Kazeem sun yi wannan taro ne a dakin Arewa House da ke Kaduna kamar yadda aka kawo rahoto a jiya.

Atiku a yankin Kudu
Taron siyasa a Delta Hoto: @ogsambassadors
Asali: Twitter

Ina amfanin mulki a Arewa

A cewar Mohammed-Kazeem, ‘yan Arewa sun yi shekara da shekaru su na rike da Najeriya, amma hakan bai iya magance talauci da rashin tsaro ba.

A taron da aka yi ranar Laraba, gamayyar kungiyoyin ta gargadi jam’iyyun siyasa da cewa ka da su ba wani mutumin Arewa tikitin takarar shugaban kasa.

Kazeem ya yi kira ga jam’iyyu su ware tutar 2023 ga ‘yan Kudu domin a kara dankon zumuncin da ke tsakanin mutanen yankin da takwarorinsu na Arewa.

Kara karanta wannan

Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari: Malaman addinin kirista a Arewa sun ce an yi musu wahayi

Lokaci ya yi da Ibo za su dana

Duk da bai cikin doka, Kazeem ya ce zai yi kyau a ba sauran bangarori damar yin mulki domin hakan zai inganta kaunar juna da ‘yanuwantaka a Najeriya.

Abin da wannan kungiya ta ke so shi ne mutumin Ibo ya zama shugaban kasa tun da yankin kudu maso yamma sun ci moriyar tikitin APC tun 2015.

Zaben APC na kasa

Bayan an yi zama a fadar Aso Rock Villa, an ji Gwamnoni sun bi umarnin Muhammadu Buhari a kan wanda zai zama sabon shugaban jam’iyya na kasa.

Babu mamaki Abdullahi Adamu ya doke Tanko Al-Makura; Sani Musa; Saliu Mustapha; Saidu Etsu; da George Akume a zaben jam'iyyar APC da za ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel