Da Duminsa: Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC Awanni Kafin Taron Gangami

Da Duminsa: Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC Awanni Kafin Taron Gangami

  • Bayan shan kaye a zaben cikin gida na takarar tikitin gwamnan APC, Lasun Yusuff, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai na tarayya ya dauki sabon mataki
  • Yusuff, a ranar Juma'a 25 ga watan Maris, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar mai mulki amma bai bayyana matakin da zai dauka a gaba ba
  • Amma, shugaban jam'iyyar APC na Jihar Osun, Kola Olabisi, bai riga ya san da batun ficewar Yusuff ba a cewar hadiminsa

Jihar Osun - Tsohon mataimakin kakain majalisar wakilai na tarayya, Mr Lasun Yusuff, ya ya murabus daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a kasa, The Punch ta rahoto.

Yusuff, ya yi takarar neman tikitin gwamna a APC yayin zaben cikin gida da aka yi, tare da gwamnan Osun mai kan mulki, Adegboyega Oyetola, da Moshood Adeoti, dan takarar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya marawa baya.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa

Da Duminsa: Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC Awanni Kafin Gangamin Taro
Tsohon Mataimakin Kakakin Dokokin Tarayya Ya Fice Daga APC Awanni Kafin Gangamin Taro. Hoto: Ade Teledalase K
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon dan majalisar ya mika takardan murabus dinsa daga APC a sakatariyar jam'iyyar da ke Osogbo a ranar Juma'a.

Ita ma Nigerian Tribune ta wallafa rahoton ficewar Yusuff daga jam'iyyar APC.

Shugaban APC na Osun bai da labarin ficewar Yusuff daga jam'iyyar

Da aka tuntube shi domin tabbatarwa, hadimin shugaban APC na Jihar Osun, Kola Olabisi, ya ce shugaban jam'iyyar ba shi da masaniya kan murabus din Yusuff.

Ya ce, "Muna Abuja. Ba a sanar da shugaban jam'iyyar cewa shi (Yusuff) ya yi murabus daga APC ba."

Amma da wakilin The Punch ya tuntube shi a wayar tarho, Yusuff ya ce:

"Na gode bisa kiran neman karin bayanin. Na bar APC. Wannan shine abin da zan ce a yanzu."

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel