Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

  • Shugaban kasa ya aikawa Atiku Bagudu takarda, ya na sanar da shi ‘yan takararsa a zaben APC
  • Akwai wadanda Muhammadu Buhari yake goyon baya su rike mukamai na kasa a majalisar NWC
  • Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki su na adawa ga ‘yan takarar shugaban kasar

Abuja - Gwamnoni da wasu cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyya su na kokarin yin fito na fito da wadanda Muhammadu Buhari ya ke goyon baya a zaben APC.

Daily Trust ta fitar da wani rahoto mai tsawo a ranar Laraba, inda aka ji cewa wadanda suke tare da shugaban kasa su na fusakantar barazana a zaben da za a shirya.

Wani jagora a tafiyar APC mai mulki ya koka kan yadda Mai girma shugaban kasa ya zabi wadanda za su rike kujeru biyar a NWC ba tare da an tunube su ba.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Rahoton ya bayyana cewa wadanda Muhammadu Buhari ya ke so a zaben da za ayi sun hada da shugaban jam’iyya na kasa da mataimakansa da kujerar sakatare.

Su wanene Buhari yake so?

Abdullahi Adamu (Nasarawa, shugaban jam’iyya), Ken Nnamani (Enugu, mataimakin shugaban jam’iyya na kudu), Ife Oluwa Oyedele (Ondo, sakatare na kasa).

Jaridar ta ce akwai Hon. Farouk Adamu Aliyu (Jigawa, mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa) da Arc Waziri Bulama (Borno, sakataren harkokin gudanarwa).

Buhari a zaben APC
Buhari da Gwamnonin APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Aikin 'Yan CPC a tafiyar APC ne

Ana zargin wasu na kusa da shugaban kasar irinsu Abubakar Malami da Malam Adamu Adamu ne suka kitsa wannan shiri sa'ilin da suka ziyarci Buhari a Landan.

Ministocin sun ba Muhammadu Buhari shawarar ya zabi wadanda za su rike jam’iyya a bayansa, don haka ya dauki shawararsu, ya sanar da Gwamna Atiku Bagudu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Legas kaddamar da ayyuka

Na kusa da shugaban kasar su na tsoron cewa idan aka tafi a haka, mutanensa na ainihi wadanda aka yi jam’iyyar CPC da su, ba za su samu komai a majalisar NWC ba.

Zaben APC, sai an tashi

Yayin da tsohon ‘dan majalisar CPC, Farouk Adamu Aliyu bai fuskantar adawa sosai. Ragowar ‘yan takarar shugaban kasar sai sun yi da gaske za su iya kai labari.

Akwai masu goyon bayan Tanko Al-Makura ya zama shugaban APC a maimakon Abdullahi Adamu.

Legit.ng ta fahimci cewa Arc. Waziri Bulama ne ya rike sakataren APC kwanakin baya. Akwai irinsu Sanata Abubakar Kyari wanda za su kawo masa cikas a zaben.

Kun san cewa gwamnonin kudu maso yammacin kasar su na tare da Duerimini Isaacs Kekemeke a zaben APC, kuma ba su goyon bayan Ife Oyedele ya zama sakatare.

Alamu na nuna gwamnonin Yarbawa ba su goyon bayan na-kusa da Buhari da Bola Tinubu. Hon. Duerimini Kekemeke ne ‘dan takararsu na mataimakin shugaban APC.

Kara karanta wannan

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

Asali: Legit.ng

Online view pixel