Gawurtattun ‘Yan siyasa 12 da za su iya neman takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2023

Gawurtattun ‘Yan siyasa 12 da za su iya neman takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2023

  • A daidai lokacin da ake ganin zaben 2023 ya gabato kusa, ‘yan siyasa sun fara buga gangunansu
  • Akwai mutane fiye da 10 da alamu suka nuna cewa za su iya neman takarar gwamna a jihar Kano
  • Kowanensu zai so ya maye gurbin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda yake kan mulki tun 2015

Jaridar 21st Century Chronicle ta kawo jerin wadannan ‘yan siyasa kamar haka:

1. Barau Jibrin

Sanata Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen neman takarar gwamna a jam’iyyar APC kafin a samu rikicin gida.

2. Nasiru Yusuf Gawuna

Nasiru Yusuf Gawuna wanda yanzu yake rike da kujerar mataimakin gwamnan zai iya shiga takarar 2023. Gawuna yana cikin manyan ‘yan siyasa da suka fito daga birni.

3. Murtala Sule Garo

Kara karanta wannan

Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023

Kwamishinan kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo yana cikin masu iko a gwamnatin Ganduje. Irinsu mai dakin gwamna na ganin matashin ne za a ba takara a APC.

4. Kabiru Alhassan Rurum

Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum babban ‘dan siyasa ne wanda yake tare da jama’arsa. Jaridar ta ce tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ya taba rike Kansila a Legas.

5. Inuwa Waya

Ku na da labari cewa Barista Inuwa Waya ya ajiye aikinsa a NNPC ne saboda ya yi takarar gwamnan Kano. Waya yana da kudin da za a gwabza da shi wajen neman tikitin APC.

6. Kabiru Gaya

Wani Sanata mai kwallafa a rai a kujerar gwamna tun ba yau ba shi ne Kabiru Ibrahim Gaya. A 1992/93, Gaya ya rike Gwamnan Kano, bayan nan ya saba da majalisar dattawa.

Manyan APC
Shugabannin APC da jagororinta a Kano Hoto: @bunimedia
Asali: Twitter

7. Abdulsalam A. Zaura

Abdulsalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da AA Zaura ya nemi gwamna a karkashin GPN a 2019. A yau ya na cikin masu tallafawa APC da mutane da dukiyarsa a Kano.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki

8. Muhuyi Rimin Gado

Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda shi ma lauya ne zai yi takara a 2023. Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci na Kano ya raba jiha da Ganduje, har ya shiga PDP.

9. Mu’azu Magaji

Injiniya Mu’azu Magaji ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna bayan sauya-shekarsa zuwa PDP. A dalilin rasuwar Abba Kyari ne ‘Dan Darauniya ya rasa kujerar kwamshina.

10. Muhammad Ibrahim Little

Har Muhammad Ibrahim Little ya saye fam domin takararar gwamna a jam’iyyar PDP. Little ya so ya yi gwamna a 2003, amma ya sha kashi a hannun Ibrahim Shekarau a ANPP.

11. Sha’aban Ibrahim Sharada

‘Dan majalisa mai wakiltar Birni da kewaye, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya ayyana shirin takarar gwamna. Sharada yana cikin ‘yan bangaren da ke adawa da Ganduje.

12. Abba Kabir Yusuf

Injiniya Abba Kabir Yusuf ne wanda ya yi wa PDP takara a zaben 2019. Alamu su na nuna Abba Gida Gida zai koma jam’iyyar NNPP domin ya sake yin takarar gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Sauran wadanda ke neman kujerar sun hada da irinsu Janar Ibrahim Sani, Kawu Sumaila da Jafar Sani Bello.

Rikicin APC

A makon da ya wuce ku ka ji cewa ana jita-jitar, an kori John James Akpanudoedehe daga matsayinsa na sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa.

Kusan duka shugabannin kwamitin riko da shirya zabe na CECPC su ka sa hannu a tsige Sanata Akpanudoedehe yayin da Gwamna Mai Mala Buni ya je kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel